
Ilmin Sakandare a Najeriya







Gwamnatin Neja na tantance malamai don inganta koyarwa. An karrama tsoffin dalibai kamar Abdulsalami da Sani Bello a taron tsoffin daliban GSS Bida.

Gwamnatin Kwara ta ɗauki mataki kan malamar da ta ci zarafin wata 'yar bautar kasa (NYSC), inda aka rage matsayin aikinta tare da tura ta wata makaranta daban.

Majalisar wakilai ta bukaci ma'aikatar ilimi ta duba yiwuwar aiki da harshen uwa a makarantun boko. Hakan zai sa a dawo amfani da Hausa a makarantun Arewa.

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya amince da biyan kudaden alawus ga shugabannin makarantun sakandare duk wata domin kula da makarantunsu.

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da fara ba da ilimi kyauta har zuwa matakin sakandare daga Janairu 2025, domin inganta ilimi ga dukkanin yara a jihar.

Gwamnatin tarayya ta hannun ministan ilmi, Tunji Alausa, ta sauya tsarin kayyade shekarun shiga jami'a na shekara 18. Ta ce tsarin koma baya ne ga harkar ilmi.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayar da kyautar makarantar sakandare ta Musulunci ta Rikadawa, wadda gidauniyar Kwankwasiyya ta gina ga gwamnatin jihar Kano.

Jami’an ‘yan sandan jihar Bauchi sun kama wasu daliban makarantar sakandare biyu bisa zargin satar wayoyin hannu guda 100 da na’urorin lantarki a wani shago.

Makarantar Firamare ta Okugbe, Ikpide-irri, tana da malami daya tilo da ke koyar da dalibai sama da 170 wanda ya sa al'ummar yankin suka garzaya ofishin gwamnati.
Ilmin Sakandare a Najeriya
Samu kari