Kano Wasu Jihohin Najeriya Za Su Samu Ruwan Sama Yau Litinin, in ji NiMet

Kano Wasu Jihohin Najeriya Za Su Samu Ruwan Sama Yau Litinin, in ji NiMet

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama mai haɗe da tsawa a wasu jihohin Najeriya da suka hada da Borno, Taraba, Kaduna
  • Ruwan na iya zuwa da iska mai ƙarfi da kuma walƙiya, wanda hakan ke zama barazana ga matafiya da waɗanda ke fakewa a ƙarƙashin bishiyoyi
  • A rahoton hasashen yanayin na ranar Litinin, NiMet ta gargadi masu ababen hawa da su yi tuƙi cikin natsuwa saboda kauce wa hadurra

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar kula da hasashen yanayi ta ƙasa (NiMet) ta fitar da rahoton yadda yanayi zai kasance a faɗin Najeriya a yau Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.

Tun a Fabrairun wannan shekarar ne dai aka fara samun ruwan sama a wasu jihohin Najeriya, kuma ana sa ran ruwan zai ci gaba da sauka har zuwa wajejen Oktoba / Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kashe Naira tiriliyan 1.1 a Kaduna, Uba Sani ya yi bayani

Ana hasashen cewa ruwan sama zai sauka a Kaduna da wasu jihohin Najeriya yau Litinin.
Wani direban Keke Napep yana tafiya a kan titi yayin da ake sheka ruwan sama. Hoto: Puneet Vikram Singh via Getty Images
Source: Getty Images

A hasashen yanayi na yau Litinin da NiMet ta wallafa a shafinta na X a daren ranar Lahadi, 3 ga Mayun 2026, hukumar ta ce akwai jihohi da dama da za su samu ruwan sama.

Hasashen yanayi a Arewacin Najeriya

A safiyar Litinin, ana sa ran samun yanayin rana tare da ɗan hazo a sassan jihohin Borno, Yobe, da Jigawa. Wannan yanayi na iya rage nisan gani a wasu wuraren, musamman ga direbobi.

A Abuja da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya kuwa, ana sa ran safiyarsu za ta kasance da yanayin rana tare da ɗan gajimare. Sai dai, ana iya samun ruwan sama mai hade da tsawa a wasu sassa na shiyyar.

A yammacin Litinin, NiMet ta ce za a iya samun ruwan sama hade da mai tsawa a jihohin Borno, Taraba, Adamawa, Gombe, Bauchi, da Kaduna.

Wannan ruwan sama na iya zuwa da iska mai ƙarfi da walƙiya, wanda zai iya zama barazana ga matafiya da kuma masu kokarin fakewa ruwa a karkashin bishiyoyi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karyata jita jita, ya jero ayyukan da gwamnatinsa ke yi a yankin Arewa

Hakazalika, ana sa ran Abuja da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya, ciki har da Plateau, Nasarawa, da kuma Niger za su samu ruwan sama da yammacin Litinin.

Hasashen ruwan sama a Kudancin Najeriya

Ana shawartar mazauna waɗannan yankuna da su tsara ayyukansu na waje duba da yiwuwar samun iska mai ƙarfi.

A shiyyar Kudancin Najeriya kuwa, NiMet ta ce za a wayi gari da hadari, amma za a samu fitowar rana a wasu sassa. Yanayin zai sauya zuwa ruwan sama mai matsakaicin karfi idan yamma ta yi.

Jihohin da ake sa ran za su samu ruwan sama sun haɗa da Oyo, Ogun, Ondo, Legas, Cross River, da Akwa Ibom. Wannan ruwan sama na iya haifar da ambaliya a wasu wuraren.

NiMet ta yi hasashen ruwan sama zai sauka hade da iska mai karfi da tsawa.
Ruwan sama na sauka tare da iska mai karfi, wanda ya jawo datti ya mamaye kan titi. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

Muhimman shawarwari da 'yan Najeriya

Hukumar NiMet ta fara yin gargadi da cewa ruwan sama na iya zuwa hade da iska mai karfi, wasu lokutan har da tsawa, wanda zai kawo tsaiko ga al'amuran yau da kullum.

An shawarci masu ababen hawa da su yi tuki cikin nutsuwa yayin da ake ruwan sama, domin ganinsu zai ragu, kuma santsin hanya na iya jawo hadurra.

Kara karanta wannan

Za a sheka ruwa yau Laraba, NiMet ta hango matsala a Kano da wasu jihohin Arewa

NiMet ta shawarci mutanen da ke zaune a garuruwan da suka saba fuskantar ambaliyar ruwa da su zauna a cikin shiri, su kuma dauki matakan kare rayuka da dukiyoyinsu.

Karanta rahoton NiMet a nan kasa:

Ambaliya: Gwamnati ta gargadi jihohi

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnati ta yi hasashen ambaliya a jihohi bakwai da garuruwa 25, inda ta gargadi mazauna bakin kogin Jebba zuwa Lokoja.

Sanarwar ta bayyana cewa jihohin da abin zai shafa sun hada da Benue, Borno, Gombe, Kebbi, Nasarawa, Neja da kuma Yobe.

Hukumar NEMA ta yi kira ga mazauna wasu garuruwan Kebbi, Neja da Kwara da su kaura daga gidajensu don kare kai daga ambaliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com