Tashin Hankali: Mutane Sun Tsere daga Garuruwan Zamfara Saboda Wani Matakin Soja

Tashin Hankali: Mutane Sun Tsere daga Garuruwan Zamfara Saboda Wani Matakin Soja

  • Fiye da kauyuka 30 ne suka koma tamkar kufai bayan da mutane suka tsere daga gidajensu sakamakon janyewar dakarun sojoji a Zamfara
  • Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa an kwashe sojojin, wadanda suka kwashe shekaru bakwai suna ba yankin kariya saboda wasu dalilai
  • Ko da yake rundunar ‘yan sanda ta ce ta tura wasu dakarun na musamman yankin, sai dai, mutane sun tattara kayansu sun arce saboda tsoro

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zamfara – Tsoro da fargaba sun mamaye sassan jihar Zamfara bayan da aka janye sojoji daga kauyen Lilo da ke gundumar Mada.

An ce janyo sojojin ya tilasta wa daruruwan mutane daga kauyuka fiye da 30 tserewa daga gidajensu domin tsira da rayuka da dukiyoyinsu.

Fargabar harin 'yan bindiga ya tilasta mutane tserewa daga garuruwansu a Zamfara
Wasu mata kenan da suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira a Borno. Hoto: Stefan Heunis/Getty Images
Source: Getty Images

Zamfara: Mutane sun tsere daga garuruwansu

Mazauna yankin sun bayyana cewa wannan hijira ta faru ne bayan da aka kwashe dakarun da aka girke a yankin tun a Yunin 2019, inda ake fargabar zaman lafiyar shekaru bakwai ya zo karshe, in ji rahoton daily Trust.

Kara karanta wannan

Miyagun 'yan daba sun kai farmaki fitacciyar kasuwar wayoyin hannu a jihar Kano

Wani mazaunin kauyen Lilo wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa janyewar sojojin ya bar su cikin fargabar harin ramuwar gayya daga ‘yan bindiga.

A cewarsa:

“Mun tsere daga gidajen mu ne saboda muna tsoron harin ‘yan bindiga da ka iya faruwa a kowane lokaci. Wadannan dakarun ne kadai kariyarmu na tsawon shekaru, yanzu kuma an janye su.”

Dalilin janye sojoji a yankin Zamfara

Akalla mutane 2,000 ne daga garuruwan yammacin karamar hukumar Tsafe ne suka tsere daga gidajensu, kamar yadda rahoton Leadership ya nuna.

An ga 'yan kauyen Kunchin Kalgo da makwabtansu na tattara ya-nasu-ya-nasu suna arcewa zuwa kwaryar karamar hukumar don neman mafaka.

A cewar majiyoyin tsaro, an janye jami’an ne wadanda yawansu ya haura 60 sakamakon kalubale na yanayi da kuma dabarun yaki.

Daya daga cikin jami’an tsaron ya bayyana cewa an janye su ne saboda fargabar harin kwanton bauna da ‘yan bindiga ke iya kai musu, musamman yanzu da damina ta kawo jiki.

Majiyar ta tuna cewa:

“A daminar da ta gabata, an dana wa sojoji tarko a wannan yankin, inda jami’ai shida suka rasa rayukansu saboda dauki ya kasa isa gare su a kan lokaci sakamakon lalacewar hanyoyi.”

Kara karanta wannan

Gobara ta lalata dukiyar miliyoyin Naira a gidan Sarki a Abuja

Rundunar 'yan sandan Zamfara ta ce ta tura jami'ai na musamman domin bada tsaro a yankin da aka janye sojoji.
Taswirar jihar Zamfara, inda mutane suka tsere daga garuruwa 30 saboda fargabar 'yan bindiga. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Martanin rundunar 'yan sanda

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sanda, A.M. Bello, ya dauki matakin gaggawa.

DSP Yazid Abubakar ya ce an tura dakarun 'yan sanda na musamman tare da motocin yaki guda biyu (APCs) zuwa yankin don ci gaba da basu kariya.

Duk da wannan tabbaci daga hukuma, mazauna yankin da dama sun bar garuruwansu, suna ganin cewa girke sojojin na dindindin ne kawai zai tabbatar da tsaro a gare su.

Mutane sun bar gidajensu a Gombe

A wani labari, mun ruwaito cewa, kimanin mutane 6,000 ne suka tsere daga gidajensu a Gombe sakamakon hare-haren 'yan bindiga da suka lakume rayuka.

Hare-haren 'yan bindiga ya shafi Garin Galadima da wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Akko, inda jama'a suka yi hijira domin tsira da rayukansu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa harin na baya-bayan nan ya afku ne a ranar 23 ga watan Janairu, 2026 wanda ya tilasta musu barin garuruwansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com