A Karshe, Gwamma Diri Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC Mai Mulkin Najeriya

A Karshe, Gwamma Diri Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC Mai Mulkin Najeriya

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta kara karfi da Gwamna Douye Diri ya sauya sheka zuwa cikin ta a hukumance yau Litinin, 3 ga Nuwamba, 2025
  • Gwamna Diri, wanda ya bar PDP makonni biyu da suke shige, ya samu tarba daga manyan jagororin APC da magoya baya a birnin Yenagoa
  • Dubban magoya bayan APC da na Gwamna Diri daga lungu da sako na kananan hukumomin Bayelsa sun halarci taron da aka shirya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa, Nigeria - Kamar yadda aka tsara, Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a yau Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Daga shiga APC, Gwamna Diri ya yi wa Tinubu alkawarin kaso 99 na kuri'u a zaben 2027

Rahotanni sun nuna cewa Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa ya cika makil yayin da shugabannin APC suka karbi Gwamna Douye Diri zuwa cikin jam'iyyar a hukumance.

Manyan jiga-jigan APC a Bayelsa.
Hoton jagororin APC da suka je tarbar Gwamna Douye Diri a jihar Bayelsa Hoto: Bonny Innocent
Source: Facebook

Dubban magoya baya sun cika Bayelsa

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa tun da sanyin safiya, misalin karfe 8:00 na safiyar yau Litinin,agoya bayan Gwamna Diri daga lungu da sako suka fara shiga birnin Yenagoa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dubban magoya bayan APC da na Gwamna Diri, sanye da riga farare da kayan al’ada masu launuka, daga kananan hukumomi takwas na jihar Baylesa sun halarci taron.

Haka nan an ga wasu magoya bayan mai girma gwamna na rera waka da rawa tare da kida da ganguna a manyan titunan birnin.

Jama'a sun cika filin tarbar Gwamna Diri

Tun da karfe 10:00 na safe, filin wasan Samson Siasia Stadium mai daukar mutum 5,000 ya cika makil da mutane.

An ruwaito cewa sai da jami’an tsaro suka dakatar da kara shigar mutane cikin filin wasan saboda gudun kada a samu cunkoso ko ko turmutsitsin da ka iya jawo asarar rayuka.

Diri, wanda ya fice daga jam’iyyar PDP kimanin makonni biyu da suka gabata, ya tabbatar da jita-jitar da ake yi ta hanyar shiga jam’iyyar APC a hukumance yau Litinin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Bayan PDP ta dare 2, kallo ya koma kan iko da hedkwatar jam'iyyar

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya jagoranci karbar Gwamna Diri zuwa APC a Yenagoa.

Jiga-jigan APC da suka tarbi Douye Diri

Taron ya kuma samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban, ciki har da Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno; Gwamnan Delta, Elder Sheriff Oborevwori.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa an ga tsohon gwamnan jihar, Sanata Ifeanyi Okowa; Gwamnan Ondo, Orimisan Aiyedatiwa; tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole a wurin taron.

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa.
Hoton Gwamna Douye Diri a wurin wani taro a jihar Bayelsa Hoto: Douye Diri
Source: Facebook

Ministan Harkokin Raya Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh, na daga cikin jami'an gwamnatin tarayya da suka isa Yenagoa don halartar bikin tarbar sabon dan APC watau Gwamna Diri.

Me yasa Gwamna Diri ya bar PDP?

A baya, mun kawo maku labarin cewa Gwamna Douye Diri ya ce ba dole ba ne kowane dan jihar Bayelsa ya fahimci dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP a yanzu.

Gwamna Diri ya bayyana cewa ya yanke shawarar fita daga PDP ne saboda maslahar jihar Baylesa, ba don son rai ko wani kwadayi na karan kansa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kusan N5bn don wasu muhimman ayyuka

Ya jaddada bukatar hadin kai, inda ya shawarci ‘yan siyasa su guji siyasar gaba da fitina, su mayar da hankali kan hadin kai da ci gaban jihar Bayelsa da kasa baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262