Bidiyon Manyan Makaman Yaki da 'Yan Ta'adda da aka Kera a Najeriya
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta koma ga kamfanin cikin gida yayin da ‘yan ta’adda ke kara amfani da jirage marasa matuka da bama-bamai daban-daban
- Kamfani Terra da Najeriya ke marawa baya ya kaddamar da sababbin jirage marasa matuka da na’urorin cire bama-bamai domin amfanin sojojin kasar
- Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan ta’adda ke kara kai hare-hare ta hanyar amfani da bama-bamai da ake birne su a kasa da wasu makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Najeriya na kokarin rage dogaro da kayan tsaro da ake shigo da su daga kasashen waje, yayin da kamfanin Terra ke shirin fadada ayyukansa zuwa Ghana domin kaiwa kasuwannin Afirka baki daya.
A ranar Litinin, kamfanin Terra ya gabatar da jirage marasa matuka masu katse hare-hare, na’urorin cire nakiyoyi ba tare da mutum a ciki ba da sauransu.

Source: Twitter
Rahoton Businees Insider Africa ya nuna cewa sauran makaman sun hada manhajojin tattara bayanan filin daga, wadanda jami’ai suka ce za su taimaka wa sojoji wajen yakar ‘yan ta’adda.
Amfani kera makamai a Najeriya
An bayyana cewa kaddamar da makaman na nuna yadda Najeriya ke kara kokari wajen gina masana’antar tsaro ta cikin gida da rage dogaro da kayan aikin soja daga kasashen waje.
Shekaru da dama Najeriya na sayen jiragen sama, motocin yaki da kayan sa ido daga kasashe irin su China, Turkiyya, Pakistan da Amurka.
Sai dai jinkirin sayo kayan, matsalolin gyara da kula da su, da kuma tsadar kudin waje sun kara nuna muhimmancin samar da wadannan kayayyaki a cikin gida.
A baya, kamfanin Terra na mai da hankali ne kan jirage marasa matuka na farar hula da fasahar tsaro kafin ya fadada zuwa bangaren kayan soja.
Ga bidiyon makaman da Reuters ta wallafa a X:
Bayanin Terra kan kera makamai
Shugaban kamfanin Terra, Nathan Nwachukwu ya bayyana cewa sun samar da makamai kala-kala domin taimakawa dakarun Najeriya.
Ya ce:
“Mun gabatar da sababbin kayan tsaro irin su jiragenmu masu katse hari, na’urorin cire nakiyoyi, motocin kasa da ke gano bama-bamai, da kuma manhajojin tattara bayanan filin daga.”
Bayanin rundunar sojin Najeriya
Shugaban kamfanin sojoji na DICON, Manjo Janar Babatunde Alaya ya ce hadin gwiwa da Terra na da matukar muhimmanci ganin yadda dakaru ke fuskantar asarar rayuka sakamakon bama-bamai da ake birnewa a kasa da gefen hanya.

Source: Twitter
Yanzu ana ganin hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu a matsayin hanya mafi sauri wajen inganta kirkire-kirkire da fadada samar da kayan aiki.
An kai hari da makamai Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan bindia dauke da makamai sun kai farmaki karamar hukumar Rogo a jihar Kano cikin dare.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa 'yan ta'addan sun kashe mutum daya cikin masu sa-kai domin tabbatar da tsaro a yankin.
Wani mazaunin yankin da abin ya faru ya yi karin bayani kan yadda maharan suka shiga garin tare da cewa sun jikkata mutane da dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


