Sanata da Ya Shirya Neman Gwamna Ya Burma Matsala, Ana Neman Yi Masa Kiranye

Sanata da Ya Shirya Neman Gwamna Ya Burma Matsala, Ana Neman Yi Masa Kiranye

  • Mata da matasa sun gudanar da gangami domin nuna rashin jin daɗinsu kan jagorancin Sanata Shehu Buba
  • Masu zanga-zangar sun ce Sanata Shehu Buba ya gaza wajen samar wa matasa aikin yi da kuma aiwatar da manyan ayyukan
  • Daya daga cikin jagororin matasan, Kwamared Saminu Tilderians shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Toro, Bauchi - A safiyar yau Talata 28 ga watan Afrilun 2026, mata da matasan karamar hukumar Toro sun yi gangami game da siyasar Sanata Shehu Buba.

Matasan sun gangamin ne na kiranye da jan hankali ga Sanatan saboda abin da suka kira gazawa a kan wasu muhimman abubuwa.

Matasa sun caccaki jagorancin Sanata Shehu Buba
Dandazon matasa mata da maza da suka yi taron gangami game da jagorancin Sanata Shehu Buba. Hoto: Comr. Saminu Tilderians, Haske No Shaking.
Source: UGC

Mai magana da yawun mata da matasan kuma shugaban matasa, Kwamred Saminu Tilderians shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa.

Kara karanta wannan

OPEC+: UAE ta dauki mataki 1 da ya girgiza Saudiyya da kasuwar mai ta duniya

Sanata Buba ya sayi fom din takarar gwamna

Wannan gangami na zuwa a ranar da Sanata Shehu Buba da ke wakiltar Bauchi ta Kudu ya sayi fom din takarar gwamnan Bauchi.

Sanatan ya ware N50m kamar yadda APC ta fitar domin shiga jerin wadanda za su nemi takarar gwamnan Bauchi, kamar yadda yaronsa, Haske No Shaking ya wallafa a Facebook.

Har ila yau, a APC akwai ministocin Bola Tinubu guda biyu, Yusuf Maitama Tuggar da Mohammed Ali Pate su ma suka nuna sha'awar neman kujerar gwamna.

An yi gangamin kin amincewa da jagorancin sanata

Saminu ya bayyana cewa a kakan zabe na shekarar 2023 an gudanar da yakin neman zabe da alkawaura da dama da ba a cika su ba.

A cewar mata da matasan, sun yi korafi da kira ga Sanata Shehu Buba cewa ya gaza wajen samar wa matasa da aikin yi.

Har ila yau, suka ce ya gaza wajen ayyukan raya karkara inda suka yi kira cewa babu wasu manyan ayyuka da za a nuna da sunan ayyukan sanatan.

Kara karanta wannan

Iran ta gana da Rasha, Putin ya yi wa Tehran alkawari kan yaki da Amurka

Kwamred Saminu ya wallafa bidiyon gangamin a Facebook inda ya ce babu abin kirki da sanatan ya yi a duk fadin karamar hukumar Toro, ban da kwalta guda daya da ya samo daga gwamnatin tarayya.

An bukaci Sanata Shehu Buba ya gyara siyasarsa a Bauchi
Shugaban matasa, Saminu Tilderians da mutanensa yayin gangami a karamar hukumar Toro. Hoto: Comr. Saminu Tilderians.
Source: UGC

Bukatun matasa ga Sanata Shehu Buba

Bugu da kari, matasan sun yi nuni da cewa an bar matasa a baya musamman a tafiyar Sanata Shehu Buba domin babu wani abu da aka yi don gina goben matasa.

Matasan sun tura bukatu ga sanatan domin dawo da martabarsa a idonsu inda suka ja hankalinsa kan ci gaban matasa da samar da aikin yi.

Daga cikin bukatunsu akwai ayyukan raya karkara, inganta rayuwar mata da matasa da aikin yi ko jari damin dogaro da kansu.

Sannan sun bukaci sanatan ya dauki alkawari bude kofar mika koke-koken al'umma domin inganta rayuwar yan mazabarsa.

Sanata Shehu Buba ya gina babban masallaci

A baya, an ji cewa Sanata Shehu Buba Umar ya gina katafaren masallaci, makarantar islamiyya da wurin ibada na musamman domin mata a jihar Bauchi.

Shehu Buba ya gode wa Allah bisa kammala aikin, yana mai cewa ya gina masallacin ne domin taimakawa wajen yada musulunci.

Malaman da suka halarci bude masallacin sun yaba wa sanatan bisa yadda yake taimakon addini, wanda hakan zai amfane shi a lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.