Majalisar Kano Ta Yi Hukunci kan Murtala Garo da aka Nemi Ya Zama Mataimakin Abba

Majalisar Kano Ta Yi Hukunci kan Murtala Garo da aka Nemi Ya Zama Mataimakin Abba

  • Rahotanni sun nuna cewa majalisar dokokin jihar Kano ta tantance Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamnan Kano
  • Tun da farko dai dama majalisar ta sanar da cewa a yau Litinin, 27 ga watan Fabrairun 2026 za ta tantance Garo bayan tura sunan shi
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sanar da cewa ta zabi Murtala Garo a matsayin sabon mataimakin gwamna ne bayan nazari mai zurfi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa siyasar jihar Kano ta shiga sabon babi bayan tantance Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamna.

Garo na cikin manyan 'yan siyasa da aka rika tattaunawa a kan su yayin da Abba Kabir Yusuf ya fara maganar wanda zai dawo masa mataimaki.

Kara karanta wannan

Gobara ta lalata dukiyar miliyoyin Naira a gidan Sarki a Abuja

Murtala Sule Garo
Murtala Garo da majalisar Kano ta tantance. Hoto: Murtala Sule Garo. Hoto: Murtala Sule Garo
Source: Facebook

Majalisar Kano ta tantance Murtala Garo

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da tantance Murtala Garo da majalisar Kano ta yi ne a wani sako da hadimin Abba Kabir Yusuf, Ibrahim Adam ya wallafa a Facebook.

Sanarwar da Ibrahim Adam ya fitar ta nuna cewa:

"Majalisar dokokin Jihar Kano ta kammala tantance Hon. Murtala Sule Garo tare da amincewa da shi a matsayin mataimakin gwamna, kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukata."

Batun mika sunan Garo Majalisar Kano

A makon da ya wuce, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sunan Murtala Sule Garo ga majalisar dokokin jihar domin a tantance shi tare da tabbatar da shi a matsayin mataimakin gwamna.

Punch ta wallafa cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami'in yada labaran gwamnan, Mustapha Muhammad, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Abba ya magantu kan fitsarar nuna dan kamfai da mata suka yi a Kano

An ce nadin ya yi daidai da Sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulkin shekarar 1999, wanda ya bai wa gwamna damar nada mataimakin gwamna idan gurbi ya samu.

An samu gurbin ne bayan tsohon mataimakin gwamna, Kwamared Abdussalam Gwarzo, ya yi murabus da kansa a ranar 27 ga Maris, 2026.

Abba Kabir Yusuf da tsohon mataimakinsa
Abba Kabir Yusuf da Aminu Abdulsalam Gwarzo. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, gwamnan ya bukaci majalisar dokokin jihar da ta amince da nadin da ya yi wa Garo.

Martanin majalisar Kano ga Abba

Bayan bukatar Abba Kabir Yusuf, majalisar dokokin Jihar Kano ta sanya ranar Litinin (Yau kenan) domin tantance Murtala Garo, bayan gwamna Abba Yusuf ya mika mata sunansa.

A ranar Laraba da ta wuce majalisar ta fitar da sakon ya tabbatar da cewa ta karbi takardar daga gwamna kan nadin Garo domin a tantance shi..

Majalisar ta ce:

“Majalisar dokokin Jihar Kano ta sanar da karbar takardar nadin wanda Mai Girma Gwamna ya mika domin mukamin mataimakin gwamna, domin a tantance shi tare da amincewa da shi,”

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatin Abba ce ta ba mata dan kamfai a Kano? An gano gaskiya

Dalilin zabar Garo a jihar Kano

A wani labarin, kun ji cewa wasu bayanai sun nuna cewa kwarewar Murtala Sule Garo na cikin dalilan da Abba Kabir Yusuf ya zabe shi.

A tsawon shekaru da ya yi yana aikin gwamnati, Garo ya rike mukamai da dama a jihar Kano da jam'iyyar APC ciki har da kwamishina.

Ana ganin kusancin Murtala Garo da manyan 'yan siyasa kamar tsohon shugaban APC kuma tsohon gwamna Abdullahi Ganduje na cikin dalilan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng