Ba Sauki: Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan ISWAP da 'Yan Ta'adda da Dama

Ba Sauki: Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan ISWAP da 'Yan Ta'adda da Dama

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Sojojin sun samu nasarar hallaka kwamandan ISWAP da wasu 'yan ta'adda sama da 20 yayin musayar wutar da aka yi
  • Hakazalika, dakarun sojojin sun kwato tarin makamai daga hannun 'yan ta'addan tare da cafke wani mayaki guda daya da ransa

​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kama aƙalla mayakin ISWAP guda ɗaya da rai a jihar Borno.

Sojojin sun kuma samu nasarar kashe wani babban kwamanda da aka bayyana sunansa da Abu Umar Bundi Munzir tare da wasu ‘yan ta'adda 24 a jihar Borno.

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP a Borno
Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce kwamandan rundunar Operation Hadin Kai a shiyyar Arewa maso Gabas, Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026 a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Ba Sassauci: Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan 'yan ISWAP, an kashe tantirai masu yawa

Sojoji sun dakile harin 'yan ISWAP

Kwamandan ya bayyana hakan ne yayin da yake ba da sabon bayani kan harin da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai amma ba su yi nasara ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Nasarar sojojin ta biyo bayan dakile wani harin haɗin gwiwa da aka kai wa kauyen Kukareta da ke Borno da dakarun Operation Hadin Kai suka yi.

'Yan ta'addan sun ƙaddamar da harin ne da tsakar dare a yunƙurin mamaye yankin, amma dakarun Sector 2 suka fafata da su cikin kwarewa a wani harin ramuwar gayya da aka shafe lokaci ana yi har zuwa kusan ƙarfe 3:00 na dare.

An kashe kwamandan ISWAP

Kwamandan ya ce a lokacin fafatawar, rahotanni sun nuna cewa kwamandan ‘yan ta’addan, Abu Umar Bundi Munzir, yana cikin waɗanda aka kashe yayin da dakarun sojoji suka fatattaki maharan, lamarin da ya tilastawa sauran maharan tserewa cikin rudani.

Manjo Janar Abubakar Abdulsalam ya kuma tabbatar da cewa an kashe wasu ‘yan ta’adda su 24 a aikin, wanda hakan ya sa jimillar waɗanda aka kashe ta kai mutum 25.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun toshe kofofin tsira ga 'yan ta'adda yayin da aka hallaka tsageru masu yawa

Sojojin Najeriya sun kwato makamai

“Daga bisani dakarun soji sun gudanar da bincike a filin daga, wanda ya kai ga samo dimbin makamai da alburusai, da suka haɗa da bindigogi kirar AK-47 guda 18, manyan bindigogi guda uku, bindigogin harbo jiragen sama guda biyu da makamin harba roka guda uku."

- Manjo Janar Abubakar Abdulsalam

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewarsa, sojoji biyu sun sami raunuka sakamakon harbin bindiga a lokacin fafatawar kuma tuni aka duba lafiyarsu, yayin da tayoyin wata motar yaƙi mai sulke suka lalace a lokacin musayar wuta.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda a jihar Borno.

Jiragen yaki na rundunar sojojin saman sun kai hari da makamai cikin kwarewa, inda suka ruguza gine-ginen, tare da kashe ‘yan ta’adda da dama.

Sojojin sun lalata muhimman kayayyakin more rayuwa na ta’addanci, kamar yadda tantance barnar da aka yi bayan hare-haren ta tabbatar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng