Korona Ta Dawo, Ɗan China Ya Sake Jajubo Cutar Covid 19 zuwa Najeriya

Korona Ta Dawo, Ɗan China Ya Sake Jajubo Cutar Covid 19 zuwa Najeriya

  • Gwamnati ta tabbatar da bullar cutar Covid-19, inda wani dan kasar China mai shekaru 53 ya kamu da cutar wanda ya daga hankulan al'umma
  • Sanarwar gwamnati ta tabbatar da cewa hakan ya faru ne bayan ɗan China ya dawo Najeriya daga kasarsa ta haihuwa
  • Kwamishinan lafiya a Cross River, Dakta Henry Ayuk, ya ce an gano cutar bayan an dauki samfurin majiyyacin a asibitin koyarwa na Calabar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Calabar, Cross River - Gwamnatin Cross River ta sanar da bullar cutar Covid-19 a jihar, lamarin da ya tayar da hankula.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gano cutar a jikin wani dan kasar China mai shekaru 53 dauke da ita.

An sake samun bullar cutar Korona a Najeriya
Alamar cutar Korona da ministan lafiya a Najeriya, Mohammed Ali Pate. Hoto: Federal Ministry of Health.
Source: Facebook

An sake samun bullar cutar Covid-19 a Najeriya

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Henry Ayuk, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Calabar, babban birnin jihar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An budewa jirgin Faransa wuta da zai wuce ta Hormuz da Iran ta toshe

A cewarsa, mutumin yana aiki da kamfanin Lafarge kuma ya dawo Najeriya daga China a ranar 17 ga Maris, 2026 kafin ya fara rashin lafiya.

Ayuk ya ce halin lafiyarsa ya tabarbare a wani asibiti kafin daga bisani aka mayar da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar domin karin kulawa.

Matakin da aka ɗauka game da samun cutar

A asibitin ne aka dauki samfurin gwaji tare da bin duk ka’idojin lafiya, wanda daga bisani aka tabbatar yana dauke da alamun cutar Korona.

Kwamishinan ya kara da cewa suna farin cikin sanar da cewa majiyyacin yana samun sauki a halin yanzu kuma ana ci gaba da kula da shi.

Ya bayyana cewa ma’aikatar lafiya ta shirya tsaf don tunkarar duk wani yanayi na barkewar cututtuka ba tare da haifar da fargaba ba.

Dan China da sake dawo da cutar Korona Najeriya
Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River yayin jawabi ga al'umma a Calabar. Hoto: Governor Bassey Otu.
Source: Twitter

Yadda aka dakile yaduwar cutar a baya

A cewarsa, akwai lokutan da ake samun kamuwa da cutar a boye, amma gwamnati za ta tabbatar da gano kowanne lamari da daukar matakin gaggawa.

Jami’ar lura da cututtuka ta jihar, Dakta Inyang Ekpenyong, ta ce an samar tsarin gaggawa tare da fara bin diddigin wadanda suka yi hulda da majiyyacin.

Kara karanta wannan

Bayan zuwan Amurka, kasar Musulunci za ta kafa cibiyar soji a Najeriya

Ta ce lokacin bayyanar cutar na iya kaiwa kwanaki 14, amma wannan lamari ya wuce hakan, wanda ke nuna yiwuwar ya kamu ne a cikin Najeriya, cewar Channels TV.

Haka kuma, jami’ar WHO a jihar, Dakta Yewande Olatunde, ta jaddada cewa cutar na nan, tare da kira ga jama’a su bi matakan kariya don kauce wa kamuwa.

An daure Sarki kan tallafin Covid-19

A baya, an ji cewa Sarkin Ipetumodu a Osun, Oba Joseph Oloyede, ya samu hukuncin fiye da shekara hudu a kurkukun Amurka saboda laifin karkatar tallafin Covid-19.

Kotun Amurka da ke birnin Ohio ta kuma umurce shi ya dawo da kudi kimanin Dala miliyan 4.4 tare da kwace wani katafaren gidan da ya mallaka a kasar.

Oloyede ya jagoranci wata makarkashiya da ta yi amfani da sunayen kamfanoni da jama’a wajen satar kudin tallafi da gwamnatin Amurka ta ware.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.