COVID-19: Ana samun sabbin masu korona 80,000 a kowacce rana – WHO

COVID-19: Ana samun sabbin masu korona 80,000 a kowacce rana – WHO

Direkta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Dr Tedros Ghebreyesus ya ce ana samun kimanin sabbin mutane 80,000 da ke kamuwa da kwayar cutar COVID-19 a kowanne rana tun watan Afrilu.

Ghebreyesus ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya yi a taron da ake gudanar a birnin Geneva.

An wallafa jawabin a shafin Intanet na Hukumar ta WHO.

A cewarsa, alkalluma da WHO ke da shi na nuna cewa fiye da mutum miliyan 3.5 sun kamu da COVID-19 kuma annobar ta kashe kimanin mutane 250,000.

Ana samun sabbin mutane masu korona 80,000 a kullum – WHO
Ana samun sabbin mutane masu korona 80,000 a kullum – WHO. Hoto daga WHO
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamna Tambuwal ya yi babban rashi

Ya ce, "Wannan ba alkalluma bane kawai, kowanne cikinsu iyayen wasu ne ko yayan wasu ko abokan wasu.

"Duk da cewa adadin wadanda ke kamuwa da cutar a kasashen Yammacin Turai yana raguwa, ana samun karuwar yaduwar cutar a Gabashin Turai, Afirka, Kuda maso Gabashin Asia, Amurka da Gabashin Mediterranean.

"Kowane yanki da kasa yana da banbanci kan yadda cutar ke yaduwa hakan yasa dole ko wane yanki yana bukatar hanyoyin dakile cutar da ya dace da shi.

"Sai dai barnar da annobar ke yi bai tsaya ga mace mace da kawai."

Shugaban ya ce annobar ta haifar ta tsaiko ga ayyuka masu muhimmanci da suka hada ayyukan lafiya.

A wani labari na daban, jami'an tsaro sun hana dubban yan kasuwa da masu cin kasuwa shiga kasuwar sayar da tufaffi na Kwari da ke Kano a yayin da gwamnatin jihar ta sassauta dokar kulle da ta saka a baya don dakile yaduwar korona.

Idan za a tuna Gwamna Abdullahi Ganduje a makon da ya gabata ya sanar da cewa kasuwannin Yan Kaba da Yan Lemo ne kawai aka bawa damar budewa a ranakun Litinin da Alhamis.

An kuma bawa wasu manyan kantina damar budewa domin sayar wa alumma kayan masarafi a ranakun biyu daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel