An samu mai dauke da cutar Korona a magarkamar 'yan sanda

An samu mai dauke da cutar Korona a magarkamar 'yan sanda

- Wani matashi ya koka kan tsare sa da a kayi a ofishin 'yan sanda kuma yana dauke da Korona

- Ya koka kan hakan zai iya shafar lafiyarsa da lafiyar wadanda a ka tsaresu tare

- Yayi kira ga hukumomi da su duba al'amarin da yake ciki domin killaceshi yadda ya dace

Wani sananne a kafofin sada zumunta, Ipadeola Oriyomi, ya zargi ‘yan sanda da kin sanya shi a wani kebantaccen waje bayan da an tabbatar yana dauke da cutar COVID-19, The Punch ta ruwaito.

Oriyomi wanda ya koka a shafukan sada zumunta ya ce, ‘yan sandan ofishin Maroko da ke Legas ne suka kama shi a wani gidan rawa da dare a tsibirin Victoria.

"Sun dauke mu zuwa ofishin 'yan sanda na Maroko inda muka kwana cikin dare kafin su sauya mu zuwa Oshodi Taskforce," ya watsa haka ne a shafin Instagram.

KU KARANTA: Sabon kamfanin jiragen sama na Najeriya zai fara aiki

An samu mai dauke da cutar Korona a magarkamar 'yan sanda
Hoto: The Punch
An samu mai dauke da cutar Korona a magarkamar 'yan sanda
Asali: UGC

Oriyomi wanda ke tsare a hannun Oshodi Taskforce tun ranar Litinin ya ce an gudanar da gwajin COVID-19 a kansa wanda ya bayyana yana dauke da cutar.

“Ina tsare a Oshodi Taskforce tun ranar Litinin. Sun gwada mu jiya don COVID-19. Gwajin ya fito yau kuma ya nuna ina da tabbacin cutar," inji shi.

Oriyomi ya ce an sake jefa shi cikin kurkuku ne a maimakon a kebe shi ko kuma a kai shi wani kebantaccen wuri na masu dauke da cutar ta COVID-19.

KU KARANTA: Zulum ya ba da umarnin karin likitoci 40 aiki a asibitocin Borno

Matashin ya roki hukumomi game da batun nasa ya ce sake jefa shi a cikin kurkukun zai jefa lafiyarsa da ta mutanen da ke tare da shi cikin hadari.

A wani labarin daban, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rufe makarantu saboda annobar COVID-19 zai yi tasiri mara kyau a kan ci gaba, aminci da kuma lafiyar yara a duniya, yana mai lura da cewa makarantu ba direbobin cutar ba ne, The Punch ta ruwaito.

UNICEF ta kuma yi gargadin cewa sakamakon rufe makaranta har shekara guda za a ji shi har zuwa tsara mai zuwa.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata ta ci gaba da cewa duk da kwararan shaidu da ke nuna cewa makarantu ba direbobi ne na cutar ba, an dauki matakai don tabbatar da cewa sun kasance a rufe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel