Za a kai Wadanda Suka Shirya Yi wa Tinubu Juyin Mulki Kotu, an Jero Laifuffukansu

Za a kai Wadanda Suka Shirya Yi wa Tinubu Juyin Mulki Kotu, an Jero Laifuffukansu

  • Gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda 13 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan wasu da ake zargi da yunkurin juyin mulki
  • Daga cikin wadanda ake zargin akwai wani tsohon Manjo Janar, tsohon Kyaftin na rundunar sojin ruwa, wani jami’in ‘yan sanda mai babban mukami
  • Ana zargin wadanda ake tuhumar da laifin yaki da Najeriya da kuma aikata laifuffukan da suka shafi cin amanar kasa da ta’addanci da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A watan Oktoba 2025, gwamnatin tarayya ta sanar da soke wani fareti da aka shirya domin bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai na kasar a ranar 1 ga Oktoba.

Bayan kwanaki kadan, rahotanni suka bayyana cewa soke bikin na da alaka da wani zargin yunkurin juyin mulki. Sai dai hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta karyata wannan batu.

Kara karanta wannan

Tsufa ya yi gardama: An kama tsoho dan shekara 60 na safarar bindigogi

Bola Tinubu da manyan hafsoshin tsaron Najeriya
Hafsoshin tsaron Najeriya tare da Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A ranar 31 ga Oktoba, 2025, The Cable ta ruwaito cewa an kama jami’an soji 16 a makon farko na watan bisa zargin yunkurin juyin mulki, yayin da wasu biyu suka tsere.

Batun gurfanar da masu 'juyin' mulki

Gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda 13 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan tsohon karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, tare da wasu mutane bisa zargin kitsa yaki da Najeriya.

Sauran wadanda ake tuhuma sun hada da Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana (mai ritaya), Kyaftin (NN) Erasmus Victor (mai ritaya), Ahmed Ibrahim, Zekeri Umoru, Bukar Goni da Abdulkadir Sani.

Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran za a gurfanar da su a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026 a gaban mai shari’a Joyce Abdulmalik.

Laifuffukan da aka zargin sun aikata

Ofishin Antoni Janar na tarayya ya ne ya shigar da tuhume-tuhumen tare da sanya hannun Daraktan gurfanarwar gwamnatin tarayya, Rotimi Oyedepo.

Kara karanta wannan

Yunkurin juyin mulki: Kotu ta yi umarni a saki Shehin Darika, Khalifa Zariya

Tuhume-tuhumen sun hada da laifuffukan cin amanar kasa, ta’addanci, boye bayanan tsaro da kuma alaka da kudin da suka shafi daukar nauyin ta’addanci.

A cewar tuhume-tuhumen, an zargi wadanda ake tuhuma da hada kai a shekarar 2025 domin raunana gwamnatin tarayyar Najeriya.

Hafsun tsaron Najeriya na yi wa sojoji bayani
Hafsun tsaro, Janar O. Oluyede na karfafa sojojin Najeriya. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto an ce sun hada baki da juna domin kaddamar da yaki da kasa da nufin tsoratar da shugaban kasa, laifi da doka ta tanada hukuncinsa a sashe na 37(2) na kundin hukunta manyan laifuffuka.

Har ila yau, ana zargin sun san da wani shirin cin amanar kasa da ya shafi wani Kanar Mohammed Alhassan Ma’aji da wasu, amma suka gaza sanar da hukumomi.

Tuhume-tuhumen sun ce:

“Sun san za a aikata laifin cin amanar kasa amma ba su gaggauta sanar da shugaban kasa ko wani jami’in tsaro ba.”

An umarci a saki Khalifa Zariya

A wani labarin, kun ji cewa wata kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bukaci jami'an tsaro su saki Sheikh Sani Abdulkadir Khaifa Zariya.

Kotun ta bayyana cewa rike malamin na tsawon lokaci kan zargin alaka da juyin mulki ba tare da gurfanar da shi ba laifi ne da ya saba dokar kasa.

Ta kuma umarci hukumomin EFCC, DSS DIA da bankin Ja'iz su ba shi miliyoyin Naira saboda tsare shi da suka yi da rufe masa asusun banki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng