Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Jakadan da Aka Tura zuwa Kasar Waje Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Jakadan da Aka Tura zuwa Kasar Waje Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Najeriya ta yi rashin daya daga cikin jakadun da ta tura zuwa kasashen wajen domin kula da harkokin diflomasiyya
  • Jakadan Najeriya da aka nada zuwa kasar Aljeriya, Mohammed Mahmud Lele, ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 50
  • Ma'aikatar harkojin wajen Najeriya ta yi jimamin rasuwar marigayin, wanda ta bayyana a matsayin jajirtaccen jami'i wanda ya samu kwarewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da rasuwar jakadan Najeriya da aka nada zuwa ƙasar Aljeria. Mohammed Mahmud Lele.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa marigayi Mohammes Mahmud Lele, ya yi bankwana da duniya yana ɗan shekara 50.

Jakadan Najeriya zuwa Aljeriya ya rasu
Ambassada Mohammed Mahmud Lele da aka nada zuwa kasar Aljeriya kafin rasuwarsa Hoto: Habib Baba Habu
Source: Facebook

Ma’aikatar harkokin waje ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakinta, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a shafin X ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Jakadan Najeriya a Aljeriya ya rasu

A cewar ma’aikatar, Mohammed Mahmud Lele ya rasu ne a ranar Lahadi, 19 ga Afrilu, 2026, a birnin Ankara na ƙasar Türkiye, bayan ya yi fama da jura-fatan rashin lafiya.

Ma’aikatar ta bayyana marigayi jami’in diflomasiyyar a matsayin jajirtaccen jami’i wanda ya yi wa ƙasarsa hidima tare da nuna gwaninta.

Marigayi Ambassada Lele, har zuwa mutuwarsa bayan doguwar rashin lafiya, shi ne darakta mai kula da sashen Gabas ta Tsakiya da yankin Gulf a ma’aikatar harkokin waje.

“Ambassada Lele, ƙwararren jami’in diflomasiyya ne wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi kwanan nan a matsayin zaɓaɓɓen Jakada zuwa Jamhuriyar Dimokuraɗiyya ta Aljeriya, biyo bayan tabbatar da nadinsa da majalisar dattawan Najeriya ta yi."

- Kimiebi Ebienfa

A ina aka haifi Mohammed Mahmud Lele?

An haife shi a Gamawa, jihar Bauchi, a shekarar 1976. Lele ya karanci tattalin arziki a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan ya yi aiki a ofishin jakadancin Najeriya da ke Berlin, Lomé, da kuma Riyadh.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sababbin ministoci 2 da ya fatattaki Wale Edun da Ahmed Dangiwa

“An san Ambassada Lele da zurfin ilimi, hangen nesa, da kuma jajircewa wajen ciyar da manufofin harkokin wajen Najeriya gaba."

- Kimiebi Ebienfa

An yi ta'aziyyar marigayin

Babban Sakataren ma’aikatar, Dunoma Umar Ahmed, wanda ya karɓi gawar marigayi jami’in a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, ya bayyana shi a matsayin “jami’i mai aiki tuƙuru, mai sauƙin kai, wanda ma’aikatar za ta yi kewarsa ƙwarai.”

Ma’aikatar ta ƙara da cewa rasuwarsa wani babban rashi ne ba ga iyalinsa kaɗai ba, har ma ga dukkanin al’ummar ma’aikatan harkokin waje da Jamhuriyar tarayyar Najeriya baki ɗaya.

Mohammed Mahmud Lele ya rasu
Marigayi Mohammed Mahmud Lele, jakadan Najeriya da aka nada zuwa Aljeriya Hoto: Habib Baba Habu
Source: Facebook

An birne Lele ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026 a birnin Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ma’aikatar ta miƙa ta’aziyya ga iyalinsa, abokan arziƙinsa, da kuma gwamnati da al’ummar jihar Bauchi, tana mai addu’ar samun kyakkyawan karshe da kuma ba wa waɗanda ya bari juriyar rashin da suka yi.

An yi rashi a masarautar Nupe

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi rashi na daya daga cikin masu rike da sarauta a masarautar Nupe da ke jihar Neja ta tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Iran ta sabunta makamai yayin tsagaita wuta da Amurka, tana shirin ko ta kwana

​Gwamna Umaru Bago ya yi ta'aziyya ga masarautat Nupe da kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Neja, bisa rasuwar Mahmud Abubakar da ke rike da sarautar Son Fada.

Bago ya bukaci iyalansa su ci gaba da jajircewa wajen yi wa marigayin addu’a tare da koyi da kyawawan ayyukansa na hidimtawa al’umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng