Najeriya Ta Yi Rashi, Tsohon Gwamna, NSA, Janar Mohammed Ya Rasu
- Tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa (NSA), Janar Abdullahi Mohammed (mai ritaya) ya rasu
- Iyalan Janar Mohammed sun bayyana cewa ya rasu da misalin karfe 1:00 na safe ranar Laraba a Ilorin, jihar Kwara
- Danginsa sun ce za a sanar da shirye-shiryen masa jana’iza daga baya a yau, bisa yadda addinin Musulunci ya tsara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara – Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon soja kuma tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasa, Janar Abdullahi Mohammed (mai ritaya), ya rasu yana da shekara 86.
Tuni danginsa suka fara shirye-shiryen yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tananda a yau.

Source: Facebook
Majiyar Daily Trust ta tabbatar da cewa marigayin ya rasu da misalin karfe 1:00 na safe ranar Laraba, inda dangi da abokansa suka bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin rayuwa da karatun Janar Mohammed
Rahoto ya ce an haifi marigayi Janar Abdullahi Mohammed da aka fi sani da Atoto a birnin Ilorin a shekarar 1939.
Ya yi karatu a Royal Military Academy Sandhurst da ke Birtaniya, inda ya kammala horo na soja sannan aka nada shi a rundunar sojin Najeriya a shekarar 1958.
Punch ta ce marigayin ya yi aiki a fannoni daban-daban na soji har ya zama daraktan leken asiri na soji (DMI) na kasa.
Janar Mohammed ya taka muhimmiyar rawa a juyin mulkin 1975 wanda ya kawo Janar Murtala Mohammed kan karagar mulki bayan hambarar da Janar Yakubu Gowon.
Mukamai da ya rike a cikin gwamnati
Bayan juyin mulkin 1975, an nada shi gwamnan tsohuwar jihar Benue-Plateau daga watan Yuli 1975 zuwa Maris 1976.
Daga nan ne gwamnatin soja ta Janar Olusegun Obasanjo ta nada shi daraktan hukumar tsaron kasa (NSO) a watan Maris 1976, wanda ita ce ta zama hukumar DSS a yanzu.
Ya rike wannan mukami har zuwa shekarar 1979 kafin ya yi ritaya daga soji. Bayan ritayarsa, ya shiga harkokin kasuwanci kuma ya kafa kamfanin Atoto Press a Ilorin.
Shugabannin kasa da ya yi aiki da su
A shekarar 1998, Janar Abdullahi Mohammed ya sake komawa ofis bayan da shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya nada shi a matsayin NSA, inda ya rike mukamin har zuwa Mayun 1999.
Bayan dawowar mulkin farar hula, shugaba Olusegun Obasanjo ya sake nada shi shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa.

Source: Getty Images
Ya rike mukamin har zuwa gwamnatin Umaru Musa Yar’Adua kafin ya yi murabus a watan Yuni 2008.
Daya daga cikin ’yan uwansa ya tabbatar da rasuwarsa da kalmar “Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un,” yana cewa:
“Mun rasa Janar Abdullahi Mohammed (Atoto) da misalin karfe 1:00 na safe yau. Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya ba mu hakuri, ya kuma karɓe shi cikin Aljanna.”
Mufti Hajj Umer ya rasu a Habasha
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban malaman Habasha, Mufti Hajj Umer ya rigamu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro ya gargadi Trump bayan barazanar kawo hari Najeriya, Buratai ya bada mafita
Gwamnatin kasar Habasha ta nuna damuwa kan rasuwar malamin tare da ba 'yan uwansa da dalibansa hakuri.
A Najeriya kuma, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar Hajj Umer yana cewa rasuwarsa babban rashi ne ga addinin Musulunci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

