Gumi Ya Magantu kan 'Yan Bindiga da Sojojin Turkiyya ke Shirin Zuwa Najeriya
- Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi martani kan shirin zuwan sojojin Turkiyya kasar nan
- Gumi da ya saba magana game da lamuran tsaro a kasar nan ya yi tsokaci kan yadda yake tunanin lamarin zai kawo karshen matsalar 'yan ta'adda
- Tun da farko dai gwamnatin Najeriya ta yi karin haske kan rawar da sojojin Turkiyya za su taka wajen kokarin kawo karshen ta'addanci a fadin kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya ce ya yi maraba da batun zuwan sojojin Turkiyya kasar nan.
Malamin ya yi magana ne bayan ma'aikatar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa ta hada kai da Turkiyya wajen samar da cibiyar horas da sojoji.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanin da Sheikh Gumi ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun 2026.
Ahmad Gumi na maraba da sojojin Turkiyya
Yayin maraba da zuwan sojojin Turkiyya, Sheikh Ahmad Gumi ya nuna cewa dama sun gudanar da ayyukan agaji da taimako a kasar nan a baya.
Malamin ya ce:
"Maraba da Turkiya domin hannunsu ba jinin bayin Allah. Ga kuma taimakon da suka yi na gina jami'ar Nile, da asibiti da sakandari masu yawa, ga yanka shanu duk sallah domin talaka. Kai, Alhamdulillah."
Game da rawarsu wajen kawo zaman lafiya, Gumi ya ce:
"Kuma, yanzu Boko Haram ba su da madafa na cewa suna yakar wadanda ba Musulmi ba. Su kuma 'yan bindiga, in sha Allah za a iya lurar da su ajiye makamansu."
"Muna fatan wannan ya kawo karshen wannan bala'i.
A karshe, Sheikh Gumi ya yi kira ga sauran al'umma da cewa:
"Su kuma mutane, don Allah su bar fasikanci, ko domin shi Allah na iya azabtar da al'ummah.
"Allah ya ba mu zaman lafiya. Amin."
Maganar ma'aikatar tsaron Najeriya
Da yake magana kan lamarin, ministan tsaro, Christopher Musa ya bayyana matakin a matsayin “babban ci gaba” a dangantakar tsaro tsakanin Najeriya da Turkiyya.
Punch ta rahoto ya ce:
“Mun kuduri aniyar samar da sakamako mai ma’ana wanda zai karfafa tsaron kasa tare da inganta manufar Renewed Hope,”

Source: Facebook
A ‘yan shekarun nan, Najeriya ta fadada hadin gwiwar tsaro da Amurka da wasu kasashen duniya domin kara karfin yaki da barazanar tsaro, ciki har da ta’addanci, garkuwa da mutane da fashi da makami.
Gumi ya yi kira ga JAMB
A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi kira ga gwamnati, JAMB da masu ruwa da tsaki su yi bincike kan hana wata daliba rubuta jarrabawa.
Malamin ya yi magana ne bayan rahoto ya ce wasu jami'an hukumar JAMB sun hana wata daliba shiga dakin rubuta jarrabawar UTME saboda ta sanya hijabi.
Hukumar JAMB ta fitar da sanarwar cewa wanda ya hana dalibar shiga dakin jarrabawar ma'aikacin wucin gadi ne kuma ta riga ta dauki matakin gaggawa.
Asali: Legit.ng


