Cikakken Bayani kan Sojoji 16 da Aka Tsare game da Zargin Yunkurin Juyin Mulki

Cikakken Bayani kan Sojoji 16 da Aka Tsare game da Zargin Yunkurin Juyin Mulki

  • Rundunar tsaro ta tsare manyan sojoji 16 kan zargin shirin juyin mulki a kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Majiyoyi sun bayyana cikakken bayani kan sojojin da ake zargi wanda ake tunanin shi ne dalilin sauya hafsoshin tsaro
  • Rahotanni sun nuna sojoji 14 ne daga Rundunar sojojin kasa, ɗaya daga Sojojin Ruwa, da kuma ɗaya daga sojojin Sama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa an kama manyan jami'an sojoji 16 bisa zargin shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wannan na zuwa ne yayin da bincike ke zurfi kan abin da ake kallo a matsayin yunkurin juyin mulki da aka gaza aiwatarwa.

An samu bayanai kan sojojin da ake zargi da juyin mulki
Jami'an rundunar sojoji a bakin aiki. Hoto: Audu Marte.
Source: Getty Images

Sojojin da ake zargi da juyin mulki

Rahoton Premium Times ya tattaro cewa daga cikin jami'an da ake tsare, 14 na Rundunar sojojin kasa ne, sai kuma ɗaya daga sojojin ruwa da ɗaya daga sojojin sama.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Brigadier-janar Musa Abubakar Sadiq

Birgediya-janar Musa Abubakar Sadiq wanda ɗan asalin Jihar Nasarawa, shi ne ake zargi a matsayin jagoran wannan tsari.

Sadiq ya shiga makarantar NDA a 1992, ya gama a 1997, sannan ya zama Birgediya-janar a 2019, an taba tsare shi bisa zargin karkatar da kayan tallafi da siyar da kayan soja da suka haɗa da motocin aiki.

2. Kanal M.A. Ma’aji daga jihar Niger

Kanal Ma'aji ya fito ne daga jihar Niger wanda ake zargin ya taka muhimmiyar rawa a shirin da ake zargi.

Ya rike muhimman mukamai ciki har da jagorantar 'Operation Delta Safe' da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

3. Laftanar-kanal S. Bappah daga jihar Bauchi

Laftanar-kanal S. Bappah, wanda aka haifa a ranar 21 ga Yuni 1984, ya fito daga Jihar Bauchi kuma ya yi aiki a Rundunar 'Signals Corps' ta sojojin Najeriya.

Ya samu horo a makarantar sojoji ta NDA tsakanin shekarar 2004 zuwa 2008, inda ya kasance ɗaya daga cikin daliban da suka kammala a zango na 56.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: An kara samun bayanan sojojin da ake zargin sun shirya kifar da Tinubu

4. Laftanar-kanal P. Dangnap daga jihar Plateau

An haifi Laftanar-Kanal P Dangnap a watan Afrilun shekarar 1986, ya samu horo a makarantar sojoji ta NDA daga 2004 zuwa 2008.

A shekarar 2015, an taba gurfanar da Dangnap daga Plateau saboda al'amuran yaki da Boko Haram, cewar Sahara Reporters.

Ana ci gaba da bincike kan sojoji 16 da ake zargi da juyin mulki
Ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Juyin mulki: Sauran sojojin da ake zargi

Sauran jami'an sojojin da ake zargi da hannu a shirin juyin mulki a Najeriya domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu sun hada da:

5. Laftanar-kanal A.A Hayatu daga jihar Kaduna

6. Laftanar-kanal M. Almakura daga jihar Nasarawa.

7. Manjo A.J. Ibrahim daga jihar Gombe

8. Manjo D Yusuf daga jihar Gombe

9. Manjo I Dauda daga jihar Jigawa

10. Manjo M.M. Jiddah daga jihar Katsina

11. Manjo M.A Usman daga birni Abuja

12. Kyaftin Ibrahim Bello

13. Kyaftin AA Yusuf

14. Laftanar SS Felix

15. Laftanar kwamanda D.B. Abdullahi (Sojan ruwa)

16. S.B. Adamu (Sojan sama)

Kara karanta wannan

Shirin juyin mulki: Sojoji sun bi diddigin N45bn zuwa hukumar raya Neja Delta

Hukumomi na cigaba da bincike, yayin da al’umma ke cigaba da sa ran gwamnati za ta bayyana ƙarin bayanai kan wannan zargin da ya girgiza rundunar tsaro ta ƙasa.

Juyin mulki: Sojoji sun bankado makudan kudi

Kun ji cewa sojojin Najeriya sun gano wasu biliyoyin Naira da aka fitar daga asusun raya Neja Delta a cigaba da bincike kan batun juyin mulki.

Ana zargin wasu manyan jami’an gwamnati da sojojin da ke tsare da hannu wajen raba kudin domin su cimma manufarsu.

Sai dai hukumar tsaro ta ƙaryata cewa akwai shirin juyin mulki, tana mai cewa ana yin binciken ne saboda dalili na daban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.