Babbar Magana: Shugaba Tinubu Ya Runtuma Kora, Ya Fatattaki Wasu Ministoci 2
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sallamar Wale Edun, wanda shi ne Ministan Kuɗi kuma babban ministan da ke kula da tattalin arziƙin ƙasa
- Haka zalika, sallamar ta shafi Ahmed Dangiwa, Ministan Gidaje da Ci Gaban Birane, a wani mataki da ya girgiza fadar gwamnatin tarayya
- Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ke fuskantar matsin lamba kan sauye-sauyen tattalin arziƙi da kuma tsadar rayuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Rahotonnin da ke fitowa daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami Wale Edun daga muƙaminsa na Ministan Kuɗi kuma babban ministan da ke kula da tattalin arziƙin ƙasa.
Wannan mataki ya zo ne a matsayin babban sauyi a cikin rukunin ministocin shugaban ƙasar tun bayan hawan sa mulki.

Source: Facebook
Tinubu ya kori ministoci 2 a lokaci guda
Ba Wale Edun kaɗai ba, sallamar ta shafi Ahmed Dangiwa, wanda shi ne Ministan Gidaje da Ci Gaban Birane na tarayya, in ji rahoton jaridar Daily Trust.
Wannan yunƙuri ya haifar da ce-ce-ku-ce a birnin Abuja, yayin da masana da dama ke ganin cewa hakan na da alaƙa da yadda ake sarrafa tattalin arziƙin ƙasar da kuma yadda manyan manufofin gwamnati ke tafiya.
Yayin da 'yan kasa ke kukan tsadar rayuwa, ana kallon Wale Edun, a matsayin "injiniyan" tattalin arziƙin gwamnatin Tinubu, kuma ya kasance ɗaya daga cikin na-kusa da shugaban ƙasar.
A ɓangaren Umar Dangiwa, ana raɗe-raɗin cewa an sallame shi ne sakamakon rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da wasu manyan ayyukan gidaje a ƙarƙashin ma'aikatarsa, zargin da ba a tabbatar ba.
Umarnin da Tinubu ya ba Edun, Dangiwa
Wannan sauyi na nuna cewa Shugaba Tinubu ya fara ɗaukar matakai masu tsauri wajen ganin ministocinsa sun sauke nauyin da ke kansa ko kuma su fuskanci korar "ba-zatar".
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya sanar da korar wadannan ministoci a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 21 ga Afrilu, 2026.
Sanarwar ta ce an bukaci Wale Edun da Umar Dangiwa da su mika dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsu zuwa ga ma'aikatun da suka bari, in ji rahoton Punch.

Source: Twitter
Gwamnati ta yi karin haske kan korar ministoci
Da yake yin bayani game da wannan mataki na Tinubu, Akume ya ce:
"An yi waɗannan sauye-sauye ne domin ƙarfafa haɗin kai da kuma samar da jituwa a tafiyar da gwamnati."
Ya jaddada cewa babban burin shugaban ƙasar shi ne ganin an samu ci gaba mai ma'ana a fannin tattalin arziƙi wanda ƴan Najeriya za su ji a jikinsu, daidai da manufofin "Renewed Hope Agenda."
Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi amfani da cikakken ikon da doka ta ba shi wajen gudanar da wannan garambawul.
Wale Edun ya magantu kan tallafin fetur
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, duk da karin farashin mai a kasuwannin duniya.
Ministan kudi, Wale Edun, ne ya bayyana hakan yayin wani taron na kungiyar G-24 da aka yi a watan Afrilun 2026 game da harkokin kudi.
Wale Edun ya jaddada cewa sauye-sauyen da Bola ]Tinubu ta fara a 2023, ciki har da cire tallafin mai sun kasance muhimman matakai da suka samu goyon bayan cibiyoyin kudi na duniya.
Asali: Legit.ng


