2023: Ba zan saye fam din Gwamna a Naira miliyan 21 ba, ya yi tsada inji ‘Dan takaran PDP

2023: Ba zan saye fam din Gwamna a Naira miliyan 21 ba, ya yi tsada inji ‘Dan takaran PDP

  • Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya koka a kan yadda jam’iyyar PDP ta lafta masu kudin saida fam
  • ‘Dan siyasar ya ce bai dace mai neman takarar Gwamna ya yanki fam a kan Naira miliyan 21 ba
  • Muttaqa Rabe Darma ya na ganin hakan zai sa ‘yan siyasa su shiga ofis da nufin maida kudinsu

Katsina - ‘Dan takarar gwamna a jihar Katsina, Muttaqa Rabe Darma ya yi Allah-wadai da yadda jam’iyyar PDP ta tsauwala kudin fam din neman takara.

Jaridar Vanguard ta rahoto Injiniya Muttaqa Rabe Darma yana cewa Naira miliyan 21 ya yi tsada a matsayin kudin fam din tsayawa takarar kujerar gwamna.

A cewar ‘dan siyasar, lafta kudin fam din tamkar ana fadawa ‘yan takara su nemi yadda za su saci dukiyar talakawansu ne idan har sun samu nasara a zabe.

Kara karanta wannan

Gardamar yankin da za a ba takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya kawo rigima a PDP

Muttaqa Rabe Darma wanda ya rike shugabancin hukumar PTDF a gwamnatin Umaru ‘Yar’adua ya yi wannan bayani wajen kadamar da littafin da ya rubuta.

Rahoton ya ce ‘dan siyasar ya rubuta wani littafi a game da jiharsa ta Katsina wanda aka radawa suna “Pathways to Greatness: The Katsina State of the Future”

Ya kamata ayi magana - Darma

Injiniya Darma ya shaidawa manema labarai cewa ya yi mamakin da ya ga ‘yan jam’iyyarsa ta PDP mai adawa ba su fito su na tir da tsadar kudin fam din ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muttaqa Rabe Darma
Muttaqa Rabe Darma Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

“Ta ina za a ce mai neman kujera ya biya N21m saboda kurum ya shiga takarar gwamna. N21m albashin gwamna kenan na watanni goma.”
“Ko da kudin albashin wata daya ne, wannan kudin ya yi yawa, kuma bazan iya biyan wannan kudi domin yin takarar gwamna a jiha ta ba.”

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Sanata Kwankwaso ya aikawa Jam’iyya takardar barin PDP, ya bayyana dalilansa

“Me su ke kokarin fadawa ‘yan takara? Su na nuna masu cewa su yi sata idan sun shiga ofis. Wannan rashin gaskiya ne, amma duk an yi tsit.”
“Mutane sun yi shiru, ba su ce komai a kai ba. Idan ba mu yi zanga-zanga ba, nan gaba za su kara kudin fam har sai ya kai Naira miliyan 100.”

- Muttaqa Rabe Darma

A cewar Injiniya Muttaqa Rabe Darma, mutanen kwarai ba za su iya shiga takara ba, domin sai masu uban gida za su samu kudin da za su yanki fam a PDP.

Idan kuwa mutum ya saye fam din sai ya fadi zabe, ya ce hakan ya na nufin zai tsiyace bayan nan.

PDP na fama da rikicin gida

Dazu nan aka ji cewa ‘Ya ‘ya da shugabannin jam’iyyar PDP sun samu kan su a cikin sabani a wasu jihohin kasar nan. Daga ciki akwai Legas mai yawan kuri'a.

Kara karanta wannan

Duk da Shugaban kasa ya sa baki, har yanzu APC na fama da rikicin cikin gida a jihohi

Masu ruwa da tsakin PDP a jihar Anambra sun kai kara gaban shugaban jam’iyyar PDP na kasa, su na zargin wasu 'yan majalisar NWC da shirya masu zagon-kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel