An Kama Gungun Barayin Mai da Suka Nufi Matatar Dangote a Legas
- Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da kama mutane 15 da ake zargi sun shirya yadda za su saci mai a kusa da matatar Dangote a Legas
- Wani rahoto ya nuna cewa mutane sun yi amfani da wasu kayayyaki da suka nufi satar mai ta wani waje da ake jigilar danyen mai
- An kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma'a, 17 ga watan Afrilun 2026, kuma an bayyana irin kayayyakin da aka same su da su a wajen
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Dakarun Sojin Najeriya sun kama mutane 15 da ake zargi za su saci mai a yankin Ibeju Lekki na Jihar Lagos kusa da matatar Dangote.
Rahoton da aka fitar ya nuna cewa mutanen sun yi yunkurin satar mai, inda aka kama wasu da bututu da wasu kayayyaki na musamman.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wani rahoton da Nairametrics ta wallafa, inda aka ce an fitar da shi ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilun 2026 a Abuja.
An kama barayi a matatar Dangote
Rahoton ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne da safiyar Juma’a ta hannun dakarun hedikwatar runduna ta 9 tare da hadin gwiwar bataliya ta 65, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Ya kara da cewa an cafke su ne yayin da suke kokarin hada wani bututu ba bisa ka’ida ba zuwa wurin zuba danyen mai daga wani jirgin ruwa da ke kai mai zuwa matatar Dangote.
“Jirgin ruwan na sauke danyen mai zuwa matatar domin samar da man fetur (PMS) da dizil (AGO) lokacin da aka kama wadanda ake zargin suna kokarin hada bututu zuwa wurin,”
In ji rahoton.

Source: Getty Images
Kayayyakin da aka kwato a wajensu
Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya ce aikin ya kai ga kama mutane 15 tare da kwato kayayyaki da dama da ake amfani da su wajen aikata laifin.
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai wata babbar tankar mai kirar Mack, mota kirar Lexus RX 350, da kuma Ford Ranger.
Sauran kayayyakin sun hada da injin tura mai, injin kwale-kwale mai karfin 40HP na Yamaha, da kuma bututun roba da dama.
“An ajiye wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato a hannun bataliya ta 65, yayin da ake ci gaba da bincike.
Rahoton ya jinjina wa sojoji da cewa:
“Nasarar wannan aiki na nuna kokarin da Sojin Najeriya ke yi na kare muhimman abubuwan more rayuwa da kuma dakile satar danyen mai a fadin kasar nan,”
Dangote ya je taro Amurka
A wani labarin, kun ji cewa attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya halarci wani taron tattalin arziki da bankin duniya da IMF suka shirya a Amurka.
Dangote ya yi magana kan yadda ake kawo wa kasashen Afrika cikas daga ketare wajen habaka tattalinsu, musamman wajen gina kamfanoni.
Ya kuma yi kira ga 'yan Afrika da su zama na gaba-gaba wajen zuba jari a nahiyarsu, domin a cewarsa, hakan ne kadai zai gayyato 'yan kasashen waje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

