Mataimakin Gwamna Ya Gina Sababbin Masallatai 50 don Taimakawa Addinin Musulunci a Najeriya
- Mataimakin gwamnan jihar Yobe, Alhaji Idi Barde Gubana ya gina masallatai 50 domin nuna godiya ga Allah SWT bisa ni'imar da ya masa
- Bayan masallatai, Gubana ya kuma dauki nauyin auren mata marayu 10 karkashin gidauniyarsa ta Gorbo Foundation
- Manyan mutane sun halarci bikin bude wadannan masallatai ciki har da babban limamin masallacin kasa, Farfesa Ibrahim Maqari
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yobe, Nigeria - Mataimakin gwamnan jihar Yobe, Alhaji Idi Barde Gubana, ya bude sababbin masallatai guda 50 da ya gina tare da taimaka wa marayu mata 10 da ya rike wajen yin aure a karamar hukumar Fune.
An gudanar da wannan aiki ne karkashin gidauniyarsa ta Gorbo Foundation, wadda ke tallafa wa marayu, mata da sauran masu bukata ta fuskar ilimi da walwala.

Source: Facebook
Mataimakin gwamna ya gina masallatai 50

Kara karanta wannan
"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027
Daily Trust ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan ya jagoranci bude daya daga cikin masallacin wanda ya gina a fadar Sarkin Fune.
Da yake jawabi ga manema labarai yayin kaddamar da masallacin, mataimakin gwamnan ya bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce kara kusantar da jama’a zuwa ga Allah SWT.
Gubana ya ce ya taimaka wajen aurar da marayu mata 10 ne bayan ya dauki nauyin rainonsu da karatunsu, inda suka zabi mazajen da za su aura da kansu.
Ayyukan alherin da Gubana ke yi a Yobe
Ya bayyana wannan aiki a matsayin sadaka da kuma godiya ga Allah da ya daga shi daga talaka zuwa mukamin mataimakin gwamna.
“A halin yanzu muna da sama da marayu 1,400 a karkashin kulawarmu. Muna daukar nauyinsu tun daga firamare zuwa sakandare, wasu kuma suna manyan makarantu.
"Wasu ma sun kammala karatu sun samu masoya, shi ya sa muka taimaka musu wajen yin aure,” in ji shi
Ya kuma yi kira ga attajirai da ‘yan siyasa da su rika tallafa wa marayu, su gina masallatai, tare da zuba jari a ayyukan da za su inganta rayuwar jama’a ta fuskar addini da zamantakewa.
Sheikh Maqari ya nemi a ba amare jari
Babban limamin Masallacin Kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, ya yabawa mataimakin gwamnan bisa wannan kokari, kamar yadda Independent ta ruwaito.
Sai dai ya bukace shi da ya kara taimakawa wadannan matan da aka aurar da su da jari domin su fara kananan sana’o’i a gidajensu na aure.

Source: Facebook
Ana ganin cewa wannan shiri na daga cikin muhimman matakan da ke taimakawa rage radadin rayuwa ga marayu da marasa galihu a al’umma.
Haka kuma, ana ganin irin wannan tallafi na kara inganta zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma, musamman a yankunan karkara inda ake fuskantar kalubale da dama.
Fasto ya gina sabon masallaci a Legas
A wani rahooton, kun ji cewa Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya kaddamar da masallacin da ya gina. Jihar Legas da ke Kudancin Najeriya.
Ayodele ya sanya wa sabon masallacin sunan mahaifiyar Shugaba Kasa, Bola Ahmed Tinubu, Hajiya Abibatu Mogaji.
Taron bude masallacin ya samu halartar manyan baki daga bangarorin addini, gargajiya, siyasa da nishadi, ciki har da wakilai daga sassa daban-daban na kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
