'Yan Sanda Sun Kama Matasa da Bindigogi 10, Harsasai 125 Za Su Kai wa Ƴan Ta'adda

'Yan Sanda Sun Kama Matasa da Bindigogi 10, Harsasai 125 Za Su Kai wa Ƴan Ta'adda

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu nasarar kama wata mata dauke da harsasai 124 da aka ɓoye cikin manja a titin Keffi-Abuja
  • An kuma kama wasu a Postiskum da katan 30 na maganin codeine, suna kokarin kaiwa ga ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane
  • Bincike ya bankado masu safarar makamai, aka kama bindigogi da N3,980,000, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da yaki da miyagu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Rundunar ƴan sanda ta samu gagarumar nasara a ayyukan yaki da laifuffuka, ta kama wasu da ake zargi da safarar makamai, miyagun kwayoyi da jabun kuɗi.

Kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa jami’an sashen fikira na musamman (FID-STS) sun kama wata mata, Hauwa Sani da harsasai a kan titin Keffi-Abuja.

Kara karanta wannan

Halin da Janar Tsiga ke ciki a hannun ƴan bindiga duk da karbar miliyoyi na fansa

'Yan sanda sun yi magana da suka kama masu safarar makamai a samame daban daban
'Yan sanda sun cafke wata mata da harsasai sama da 100 za ta kai wa 'yan bindiga a Katsina. Hot: @Princemoye1
Asali: Twitter

An cafke mata da harsasai 124

ACP Olumuyiwa ya bayyana nasarar kama Hauwa, mai shekaru 30 da haihuwa ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, a ranar 18 ga Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, an kama Hauwa Sani dauke da harsasai 124 da aka ɓoye a cikin galan din manja mai lita 5, kuma ta amsa cewa wani Nasiru daga Daura ne ya ba ta domin ta kai Katsina.

Rundunar ƴan sanda ta ce bincike ya zurfafa, aka samu damar kama karin wasu masu hannu a safarar harsasan tare da gano wasu kayayyakin laifi da yanzu ake bincikensu.

Sanarwar ta ce:

"Ana kira ga ‘yan kasa da su yi taka-tsantsan kuma su kasance masu lura da dabarun wadannan masu fataucin kayayyakin. Akai rahotn duk wani abu da ake zargi ga hukumomin da suka dace."

'Yan sanda sun kama dillalan kwaya

A wani samame da aka gudanar ranar 1 ga watan Fabrairu, 2025, ƴan sanda sun kama Alhaji Usman Yahaya, Joseph Matthew, da Solomon Bala a Postiskum, jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

"An kama waɗanda ake zargi yayin da suke safarar katan katan na maganin codeine guda 30 da sauran miyagun kwayoyi a yankin Postiskum."

- A cewar sanarwar ACP Olumuyiwa.

Masu laifin sun amsa cewa sun yi niyyar safarar kwayoyin ne ga ƴan bindiga, 'yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane a yankin Yobe da kasashen makwabta.

An cafke matasa dauke da bindigogi 10

Bayan wannan, ranar 3 ga watan Fabrairu, 2025, jami’an FID-STS sun kama wasu matasa uku: Yusuf Dantani, Usman Labaran, da Musa Mohammed (23) dauke da bindigogi kirar AK-47 guda 10.

A yayin bincike, wadanda aka kaman sun bayyana cewa sun dade suna safarar makamai, ana biyansu miliyoyin kudi.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu yayin bincike, suka bayyana cewa sun dade suna gudanar da harkar saye da sayar da makamai.
"Kuma sun karɓi N3,980,000 daga wadanda suke harkalla da su domin kai masu makaman da aka kama su da su a yanzu."

Kara karanta wannan

Wata mata ta rasu a wani irin yanayi yayin tafsirin Kur'ani a Abuja

'Yan sanda sun nemi taimakon 'yan kasa

'Yan sanda sun kama bindigogi 10 ana shirin kai su ga 'yan bindiga
'Yan sanda sun kama matasa uku dauke da bindigogi 10 za su kai wa 'yan bindiga. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Wadannan nasarorin da aka samu sun nuna ƙudirin hukumar ‘yan sandan Najeriya na yaki da laifuffuka, dakile ayyukan miyagu, da tabbatar da tsaron ‘yan kasa.

Sanarwar ta ce hukumar ‘yan sanda ta jaddada aniyarta na tarwatsa kungiyoyin masu aikata laifi tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

"Muna kira ga jama’a da su ci gaba da ba mu hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen dakile laifuka," inji ACP Olumuyiwa.

Duba sanarwar 'yan sandan a nan:

'Yan bangar siyasa sun kashe shugaban matasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan Imo ta tabbatar da kisan Chigozie Nwoke, wanda aka ayyana a matsayin zakaran zaben matasa a watan Janairu.

An kashe shi a ranar 15 ga Maris da misalin karfe 9:00 na dare, aka raunata ‘yan uwansa hudu tare da kona gidaje tara.

Kara karanta wannan

Gobara kashe mutane 7, ta lalata kadarorin Naira miliyan 50 a jihar Kano

‘Yan sanda na zargin wata kungiya karkashin jagorancin Chinaza Nwachukwu da kai harin, yayin da ake kokarin cafke wadanda suka tsere.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng