Kalli hotunan iyalan dan sanda da aka kashe a fashin Offa inda suka shiga halin kunci
Iyalan jami’in dan sandan da aka hallaka a mummunan harin da aka kai yankin Offa na jihar Kwara sun shiga halin dimuwa da damuwa.
A yanzu haka suna nan sun rasa inda zasu sanya ransu domin suji dadi, sannan wakilan Legit.ng sun kai masu ziyara inda suka zanta dasu akan wannan mummunan yanayin.
A ranar Juma’a, 13 ga watan Afrilu, rundunar yan sanda Najeriya sun bayyana sunayen mutane 12 da aka kama da hanu a mummunan fashin da akayi a Offa, jihar Kwara.
A halin da ake ciki, Legit.ng ta tattaro cewa binciken yan sanda ya bankado wadanda ke da hannu a fashin Offa wanda yayi sanadiyan mutuwar mutane da dama ciki harda yan sanda.
Yan fashin sun kai farmaki garin a ranar 5 ga watan Afrilu inda suka kashe mutane 17 sannan suka kai hari bankuna biyar. Yan sanda takwas a hukumar Owode, Offa na daga cikin wadanda aka kashe a harin, sannan kuma yan fashin sun tafi da makaman yan sanda.
Yan sandan sun kama mutane bakwai cikin kwanakin biyun farko da kai harin, sannan kuma daga baya suka sake wasu hare-haren.
Ga karin hotuna na iyalan marigayin:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng