Fashin Offa: ‘Yan sanda masu bincike sun biyo Saraki har Ofis

Fashin Offa: ‘Yan sanda masu bincike sun biyo Saraki har Ofis

A cigaba da sa-toka-sa-katsin dake faruwa tsakanin hukumar ‘yan sanda da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, a yau, Alhamis, jami’an ‘yan sanda masu bincike sun bi Saraki har Ofis bayan ya ki amsar gayyatar da suka yi masa.

Yayin ganawar tasu, Saraki, ya kafe kan cewar bashi da hannu a cikin fashin da aka yi tun watan Afrilu a garin Offa dake jihar Kwara.

A wani sako da Olu Onemola, mai taimakawa Saraki a bangaren yada labarai, ya fitar a yau ta shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewar babu yadda za a yi maigidan nasa ya bawa ‘yan ta’adda gudunmawa ko daurewa ta’addanci gindi.

Fashin Offa: ‘Yan sanda masu bincike sun biyo Saraki har Ofis

Bukola Saraki

Bayan hukumar ‘yan sanda ta bukaci Saraki ya bayyana a Ofishinta ranar 23 ga watan Yuli, da kuma amsa da ya aikewa masu na cewar ba zai samu damu amsa gayyatarsu ba a ranar, a yau da misalign karfe 1:40 na rana, shugaban majalisar ya gana tawagar ‘yan sanda masu bincike a ofishinsa.

“Saraki ya yi amfani da ziyarar ‘yan sandan wajen kara jaddada masu cewar bashi da nasaba da batun fashin garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu,” kamar yadda yake a sakon da Onemola ya fitar.

Tun da dadewa hukumar ‘yan sanda ta sanar da cewar ‘yan fashin Offa da ta kama sun shaida mata cewar suna yiwa Saraki aiki ne kuma tun a wancan lokacin, hukumar ta ‘yan sanda ta bukaci Saraki ya gabatar da kansa domin amsa tamboyi kafin daga bisani ta umarce shi ya aiko da jawabinsa a rubuce.

DUBA WANNAN: Cikin Hotuna: 'Yan majalisar wakilai na APC sun ziyarci shugabancin jam'iyyar, sun mika wata bukatarsu

Saidai tun a wancan lokacin, gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya bayyana cewar kuskure ne a alakanta shi da Saraki da fashi da makami.

Kazalika Saraki da kansa ya yi watsi da batun zargin da ake yi masa na hannu a cikin fashin garin Offa. Saidai har yanzu bai musanta cewar ‘yan fashin yaransa dake masa bangar siyasa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel