Peter Obi Ya Fadi Shirinsa kan Arewa, Ya Bayyana Tagomashin da Yankin Zai Samu
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Peter Obi, ya yi tsokaci kan shirin da yake da shi kan yankin Arewacin Najeriya
- Peter Obi ya bayyana cewa yana da shirin ganin ya kawo ci gaba mai yawa a Arewa saboda muhimmancin da yankin yake da shi a kasa
- Hakazalika, Peter Obi ya kuma yi magana kan hanyoyin da ya kamata a bi domin magance matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, ya bayyana shirin da yake da shi kan yankin Arewa.
Peter Obi ya bayyana cewa yana shirin ba da fifiko ga ci gaban Arewa, inda ya bayyana yankin a matsayin mafi girman kadarar da Najeriya ke da ita.

Source: Facebook
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Prime Time na tashar Arise News ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.
Me Peter Obi ya ce kan Arewa?
Peter Obi ya ce Arewa tana da damammaki masu tarin yawa na tattalin arziƙi, musamman a fannin noma, wanda ya yi amannacewa zai iya zarce kuɗin da ake samu daga man fetur idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata.
“Babbar kadararmu tana Arewa. Filayen da ba a noma su ba a Arewa sune makomarmu. Za mu iya samun kuɗi a matsayin ƙasa daga noma fiye da yadda muke samu daga man fetur, kuma dole ne mu fara yin hakan nan take."
- Peter Obi
Peter Obi zai yi aiki da 'yan siyasar Arewa
Peter Obi ya ce a shirye yake ya yi aiki da manyan jiga-jigan siyasar Arewa, ciki har da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan
Shugaba Putin ya kira takwaransa na Iran a waya, an ji abin da suka tattauna tsakaninsu
“Zan yi aiki da su, amma zan iya gaya muku cewa babu wanda zai iya gina abin da nake da niyyar gina wa a Arewa."
- Peter Obi

Source: Facebook
Me ya ce kan rashin tsaro?
Game da batun tsaro, tsohon gwamnan na Anambra ya ce magance rashin tsaro a yankin yana buƙatar yaƙi da talauci da kuma gyara matsalolin shugabanci.
“Idan muna son samar da tsaro a Arewa a yau, muna buƙatar fara zuba jari a muhimman fannoni na noma, fitar da mutane daga talauci, da kuma zuba jari a fannin ilimi da lafiya. Wannan shi ne abin da dole mu yi."
- Peter Obi
Ya ƙara da cewa dole ne shugabanci ya kasance mai tsauri wajen tunkarar rashin tsaro, yana mai lura da cewa halin da ake ciki a yanzu sakamakon gazawar shugabanci ne na shekaru da dama.
Peter Obi ya magantu kan talauci a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya yi magana kan matsalar talauci.
Peter Obi ya bayyana cewa matsalar talauci a Najeriya ba rashin albarkatun kasa ba ne, face sakamakon irin zaɓin da ƙasar ta yi ne.
A cewarsa, ainihin matsalar ita ce shugabanci da kuma al'adar da ke girmama cin hanci da rashawa maimakon yaƙarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
