Duhu zai kare: Bankin duniya zai sharewa 'yan Najeriya hawaye kan lantarki
- Bankin Duniya ya tsara haɗa ‘yan Najeriya miliyan 32 da wutar lantarki a cikin sabon tsarin haɗin gwiwa na shekarun 2026 zuwa 2032
- Tsarin zai kuma bai wa karin mutane miliyan 58 damar samun intanet, tare da tallafa wa manoma miliyan 9.5 domin inganta noma d
- Bankin Duniya ya ce zai kuma jawo sanya zuba jarin dala biliyan 4.1 domin bunkasa abubuwan more rayuwa da harkar noma a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bankin Duniya ya tsara haɗa ‘yan Najeriya miliyan 32 da wutar lantarki tare da bai wa wasu karin mutane miliyan 58 damar amfani da intanet a ƙarƙashin sabon tsarin haɗin gwiwarsa da Najeriya na shekarun 2026 zuwa 2032.
Tsarin ya kuma yi niyyar tallafa wa manoma miliyan 9.5 domin inganta noma, ƙara darajar amfanin gona da haɗa su da kasuwanni, yayin da Bankin Duniya ke shirin jawo masu zaman kansu su zuba jarin dala biliyan 4.1.

Source: Facebook
Punch ta wallaa cewa Mukaddashin Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Taimur Samad ne ya gabatar da sabon tsarin CPF ranar Laraba a Legas, yayin wani taro.
Aikin da bankin duniya zai yi
Shirye-shiryen sun hada da samar da makamashi a wurare daban-daban, bunkasa hanyoyin intanet, saukaka samun jari ga ga kanana da matsakaitan sana'o'i da kuma bunkasa harkar noma.
A cewar takardar bayanan tsarin:
"Mutane miliyan 32 za a samar wa da wutar lantarki. Karin mutane miliyan 58 za su samu damar amfani da intanet.
"Manoma miliyan 9.5 za su amfana da shirye-shiryen inganta noma, kara darajar amfanin gona da hada su da kasuwanni, yayin da za a samar da dala biliyan 4.1 daga jarin masu zaman kansu."
Rahoton MSME Africa ya ce tsarin zai samar da karin ayyukan yi masu inganci tare da kara yawan kudin shiga daga bangaren da ba na man fetur ba zuwa kashi 30 cikin 100 na GDP.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito: An gano bashi ya yi wa Amurka katutu yayin da ta ke yaki da Iran
Batun inganta kiwon lafiya
A bangaren lafiyar jama'a da ilimi, tsarin ya yi niyyar tallafa wa mutane miliyan 40 a bangarori ciki har da samar abinci mai gina jiki da sauran ayyukan raya jama'a.
Za a kuma tallafa wa dalibai miliyan 19.4 domin samun ingantaccen ilimi, tare da rage yawan yara 'yan kasa da shekaru biyar.
Haka kuma, karin mutane miliyan 41 za su amfana da shirye-shiryen tallafin jin kai, yayin da mutane miliyan 11.7 za su samu karin damar tinkarar illolin sauyin yanayi.

Source: Facebook
An rage bashin wutar lantarki
A wani labarin,mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta Najeriya ta yi nasarar fitar da kason farko na takardar lamuni ta Naira biliyan 501 a karkashin shirin PPSDRP.
Gwamnatin tarayya ta ce shirin zai taimaka wajen biyan bashin da ake bin bangaren samar da wutar lantarki, bunkasa kudin gudanarwa.
Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin zai kara kwarin gwiwar masu zuba jari a masana'antar wutar lantarki ta Najeriya.
Asali: Legit.ng
