Girma Ya Faɗi: Gwamna da Kansa Ya Tura Babban Sarki Kotu kan Zargin Damfara, Dabanci
- Gwamnatin jihar Ogun ta gurfanar da Oba Taofeek Owolabi a kotu bisa zargin kwace fili da karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba
- An zargi Oba Owolabi da damfarar wani mai saka jari, Dr Michael Adeyemi, har N75m game da filin da ba nasa ba
- Majalisar Dokokin Jihar ta nemi Oba ya bayyana, amma ya ƙi amsa, maimakon haka ya kai ƙara kotu, daga baya ya janye
- Majalisar Sarakunan Egba ta dakatar da shi a watan Disamba 2024, bayan ya ƙi amsa gayyata, kotu kuma na cigaba da shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Gwamnatin Jihar Ogun ta gurfanar da Olu na Obafemi, Oba Taofeek Owolabi a gaban Mai Shari’a Sunday Adeniyi a babbar kotun jihar.
An dakatar da ɗan majalisar gargajiya ta Egba, Oba Owolabi kan wannan zargi da ake yi masa kafin sake aikatawa.

Asali: Facebook
An tura Sarki kotu kan zargin damfara
Shafin Facebook na gwamnatin jihar Ogun shi ya tabbatar da haka a jiya Laraba 23 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, an gurfanar da shi ne kan laifin haɗin baki na sayar da fili ba bisa ƙa’ida ba da amfani da ’yan daba.
An ce Sarkin yankin ya ƙwace fili mai eka 500 a Obafemi Owode, ya damfari Dr Michael Adeyemi har N75m.
Gwamnati ta ce bai biya dangin masu filin ba, ya kuma tura ’yan daba suka yi wa mutumin duka da sara wani jami’in hukuma.
Sanarwar ta bayyana yadda gwamnatin Ogun ta yi ƙoƙarin dakatar da shi, amma ya ƙi amsa gayyatar majalisar dokoki, maimakon haka ya kai ƙara kotu.
Bayan ya janye ƙarar, bai bayyana a binciken majalisa ba, daga ƙarshe, kwamitin ya ba da shawarar a gurfanar da shi kotu.

Asali: Original
Gwamnati ya yi gargadi kan kwace filaye
Sarkin sarakunan Egba, Oba Adedotun Gbadebo, da majalisar sun gayyace shi sau da dama, amma Oba Owolabi ya ƙi bayyana.
Kwamitin ladabtarwa na majalisar gargajiya ya shiga lamarin, amma ba a yi nasara ba, hakan ya sa aka dakatar da shi ranar 13 ga watan Disambar 2024.
Sanarwar ta ce ko da yake ya cika sharudan beli, har yanzu shari’a na ci gaba, gwamnati na da niyyar ganin an yi adalci.
Gwamnati ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da aminta da ƙoƙarinta na kawo tsari wajen mallakar fili a jihar Ogun.
An ce gwamnati za ta ci gaba da yaki da masu kwace fili, ko da kuwa su wanene, ba za ta lamunci hakan ba.
Sace mutane: Gwamnan Edo ya dakatar da Sarki
Kun ji cewa Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da Sarkin Uwano, George Egabor, bisa yawaitar sace mutane da kisa a masarautarsa.
Kakakin Gwamna Monday Okpebholo mai suna Fred Itua ya fitar da sanarwa inda ta tabbatar da dakatarwar da kuma kama Sakataren Sarkin, Peter Omiogbemhi.
Hakan ya biyo bayan kama Omiogbemhi kan zargin wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar wani dattijo na fada mai suna John Ikhamate.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng