Bayan Kisan Ɗan Uwansa, ana Zargin Bello Turji na Neman Sulhu domin Miƙa Wuya

Bayan Kisan Ɗan Uwansa, ana Zargin Bello Turji na Neman Sulhu domin Miƙa Wuya

  • Rahotanni sun bayyana cewa Bello Turji yana neman a yi sulhu bayan mutuwar dan uwansa kuma kwamandansa
  • An ce Turji na shirin ganawa da wasu kungiyoyin 'yan bindiga domin duba yuwuwar mika wuya ga gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma
  • Wata majiya ta ce, Turji ba ya da karfi yanzu, Kachalla Danbokolo ne ke tafiyar da ayyukan fada da kayayyaki a daji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Majiyoyi - Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa Bello Turji yana nuna alamun sulhu bayan kashe wani na kusa da shi.

An tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da kisan hatsabibin dan bindiga kuma ɗan uwansa, Kachalla Yellow Danbokolo da jami'an tsaro suka yi.

Bello Turji ya fara neman a yi sulhu
Bello Turji na neman sulhu da gwamnati kan ta'addanci. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya ce Turji, daya daga cikin shahararrun jagororin 'yan ta'adda a Arewa na neman tattaunawa da sauran 'yan bindiga domin mika wuya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kisan Danbokolo ya faranta ran al'umma

Hakan ya biyo bayan kisan da yan sa-kai suka yi wa Kachalla Yellow Ɗanbokolo a wani artabu a jihar Zamfara.

Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da mutuwar kwamandan ƴan bindigar, wanda ake ganin ya zarce Bello Turji haɗari.

Danbokolo ya samu munanan raunuka a wani samame da DSS da HYBRID Forces suka kai a Chida, karamar hukumar Shinkafi.

Ya rasu bayan kwana uku, a ranar 26 ga Yuni, bayan an kai shi kauyuka da dama domin ceton rayuwarsa amma hakan ya ci tura.

Mazauna yankin sun fito domin bayyana jin dadinsu, inda suka ce suna sa ran bana babu wanda zai dora masu harajin noma.

Sun bayyana fatan gwamnati da matasan za su ci gaba da kai irin wannan farmaki, irinsa na farko mafi muni da aka kaddamar a kan 'yan ta'adda.

Mutuwar kwamandan Bello Turji ya rikita masa lissafi
An tabbatar da cewa Bello Turji na neman sulhu bayan kisan dan uwansa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Musabbabin neman sulhu da Turji ke yi

An ce wannan yunkuri na Turji na da nasaba da mutuwar Danbokolo wanda ke jagorantar hare-hare da satar mutane a jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina.

“Turji fuska ce kawai Danbokolo ne ke jagorantar fada, da kayayyaki, da kuma tsare dajin."

- Cewar wata majiya

Wasu sun ce Turji bai tuba ba ne da gaske, sai dai yana kokarin kare kansa bayan ya rasa karfin aikata laifi.

Hukumar tsaro ba ta ce komai ba tukuna, amma masana sun yi kashedi cewa ya kamata gwamnati ta bi hanyar karshe, ba afuwa ba.

"Turji bai cancanci gafara ba, Gwamnati ta yi watsi da kokarin mika wuya da ya ke yi."

- In ji wata majiya

Gwamnatin Zamfara ta ce ta fatattaki Bello Turji

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun da aka yi da ‘yan bindiga ya zama wata sabuwar hanya wajen murkushe su gaba ɗaya.

Hadimin gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Manga ya bayyana cewa an kutsa har cikin mafakar dan bindiga inda aka samu gagarumar nasara.

Gwamnatin Dauda Lawal Dare ta ce za ta ci gaba da farautar Bello Turji, yayin da aka ce ya tsere yayin artabun da aka yi da mayaƙansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.