Katsina: Ƴan Bindiga Sun Yi Shigar Dare, Sun Sace Sarki yayin Wani Farmaki

Katsina: Ƴan Bindiga Sun Yi Shigar Dare, Sun Sace Sarki yayin Wani Farmaki

  • Wasu ’yan bindiga sun kai hari cikin dare a Karaduwa da ke Matazu, Jihar Katsina, inda suka sace Hakimin garin, Alhaji Abdullahi Bello
  • Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar, 5 ga Yuli, inda suka ce maharan sun kai farmaki ba tare da tsoro ba
  • Har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, babu wani bayani daga hukumomin tsaro game da yadda lamarin ya faru ko matakin da aka ɗauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Wasu yan bindiga sun kai wani hari a cikin dare a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun farmaki al'umma a wani ƙauye da ke karamar hukumar Matazu.

Yan bindiga sun kai wani hari a daren jiya a Katsina
Yan bindiga sun sace basarake a jihar Katsina. Hoto: Legit.
Asali: Original

Shafin Bakatsine mai kawo rahotanni kan tsaro da ta'addanci shi ya tabbatar da haka a dandalin X da safiyar yau Asabar 5 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun addabi yankin Arewacin Najeriya

Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren yan bindiga wanda ya daidaita garuruwa.

Lamarin rashin tsaro ya mamaye yankin da ya haɗa Arewa maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya wanda ya jawo asarar rayuka da duniyoyi.

Duk da haka jami'an tsaro na cigaba da kakkabe yan bindiga wanda ya yi sanadin rashin manyan hatsabiban yan ta'adda a yankin.

Na hannun daman Bello Turji ya sheka barzahu

A cikin kwanakin nan, jami'an tsaro da hadin guiwar yan sa-kai sun yi nasarar hallaka rikakken dan ta'adda kuma na hannun daman Bello Turji.

An ce marigayi Kachallah Yellow Danbokolo shi ne kusan karfin Turji wanda majiyoyi ke cewa a yanzu an ragewa dan bindigar karfi.

Wasu rahotanni suka ce hakan ya sa Bello Turji fara neman mafita inda aka ce yana neman hanyar sulhu domin ajiye makami.

Yan bindiga sun sace wani Sarki a Katsina
Yan bindiga sun kai wani hari a daren jiya Katsina. Hoto: @DanKatsina50.
Asali: Facebook

An sace Sarki cikin dare a jihar Katsina

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne a kauyen Karaduwa inda suka sace Hakimin kauyen, Alhaji Abdullahi Bello.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu wata sanarwa na musamman daga jami'an tsaro kan lamarin.

Sanarwar ta ce:

"A daren jiya, ’yan bindiga sun sace Hakimin Karaduwa (Magajin Garin Karaduwa), Alhaji Abdullahi Bello Karaduwa.
"Karaduwa ƙauye ne da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Matazu a Jihar Katsina."

A jihohin Arewacin Najeriya dai an sha sace sarakunan gargajiya da kuma malaman addini wanda hakan ke kara sanya fargaba a zukatan al'umma.

Yan bindiga sun ɗauke Hakimi a Kaduna

A baya, mun ba ku labarin cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace mai unguwar Bauda da ke Maro, karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna da asuba.

Rahoto ya ce 'yan bindigar sun kai farmaki ne da misalin karfe 1:00 na dare, sun tafi da Obadiah Iguda kadai ba tare da kashe kowa ba.

Lamarin ya ta da hankalin al'umma, yayin da hukumar Kufana ta bukaci gaggawar daukar matakin tsaro domin hana sake faruwar hakan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.