'A Fara Tilasta Horon Soja ga Ƴan Najeriya': Tsohon Hafsan Sojoji Ya Kawo Mafita kan Tsaro

'A Fara Tilasta Horon Soja ga Ƴan Najeriya': Tsohon Hafsan Sojoji Ya Kawo Mafita kan Tsaro

  • Tsohon shugaban sojojin kasa, Janar Azubuike Ihejirika mai ritaya ya kawo hanyar dakile matsalolin tsaro a Najeriya
  • Ihejirika ya bukaci a fara tilasta horon sojoji ga matasan NYSC don cusa kishin kasa da kawo karshen ta'addanci
  • Ya ce matakin zai taimaka wajen hade kan al’umma da bunkasa ladabi da kwarewa, musamman a lokacin da ake fama da kalubalen tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanar Janar Azubuike Ihejirika (mai ritaya) ya ba da shawara kan matsalolin tsaro.

Janar Ihejirika ya bukaci a wajabta horon sojoji ga ‘yan Najeriya, ta hanyar farawa da NYSC domin cusa kishin kasa.

Tsohon hafsan sojoji ya kawo mafita kan matsalar tsaro
Tsohon hafsan sojoji, Janar Ihejirika ya ba da shawara kan matsalolin tsaro. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Ihejirika ya kawo mafita kan ta'addanci

Ihejirika ya yi wannan kiran ne yayin bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar tsofaffin daliban NDA Regular Course 18 a Abuja, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a matsayin hanyar karfafa hadin kan kasa, ladabi da juriyar ‘yan kasa a lokacin da ake fuskantar matsalolin tsaro da na zamantakewa.

Ya tuna da rayuwarsa lokacin da ya shiga soja da kuma irin zumuncin da suka gina tare da abokan aikinsa tsawon shekaru.

Tsohon hafsan ya ce ladabi da kishin kasa da suka koya lokacin atisaye ne ya taimaka wajen gina rayuwarsu da sadaukar da kai ga kasa.

Ya ce:

“Duba da halin da kasa ke ciki yanzu, ina ganin lokaci ya yi da za mu fara tunanin tilasta horon soja ga duk ‘yan kasa.
"Za mu iya fara daga NYSC, wannan zai taimaka wajen gina matasa masu fahimtar sadaukarwa da kishin kasa."
An shawarci sojoji yadda za su kaso karshen ta'addanci
Tsohon hafsan sojoji ya kawo mafita kan ta'addanci. Hoto: HQ Nigeria Army.
Asali: Facebook

Taken Najeriya: Ihejirika ya yabawa Tinubu

Ihejirika ya yaba da matakin gwamnati na dawo da tsohon taken kasa, yana mai cewa hakan zai karfafa hadin kai.

Ya ce layin “Ko da yare da harshe sun bambanta, hadin kanmu na tsaye” na dauke da ainihin ma’anar bautar kasa.

Ya bayyana damuwa kan yadda ake rage taken Najeriya zuwa abin kidan bukukuwa kawai a wuraren gwamnati.

“Ya kamata ya zama tunatarwa kullum kan rantsuwar da muka yi. Dole a dawo da shi makarantu, unguwanni da tarukan kasa."

- Cewar Ihejirika

Ya tuna da yadda ya taso daga kauyensu a Abia da yadda horon soja ya canja rayuwarsa zuwa nagarta.

Ya gode wa abokai da manyan hafsoshi da suka taimaka masa har ya kai matsayin shugaban hafsoshin sojin kasa na 22.

Baya ga wannan kira, Janar din ya yaba da shugabancin sojin Najeriya na yanzu, yana mai cewa sun kware sosai.

Wani matashi dan bautar ƙasa ya yi martani

Umar Mu'azu da ke gudanar da bautar ƙasa a jihar Kogi ya ce wannan ba shi ne mafita ba kan lamarin tsari ko kishin kasa.

Matashin dan asalin jihar Gombe ya ce akwai matasa da ke sha'awar aikin soja amma rashin gata ya hana su samu.

Ya ce:

"Dubban matasa na neman aikin soja duk shekara amma saboda ba su san kowa ba ba su samun dama."

Ya ce don haka, ba wadancan masu sha'awar zai wadatar ba sai an juyo kan yan Najeriya ba.

Sojoji sun dakile harin yan ta'adda

Kun ji cewa sojoji da jami'an JTF sun gano tare da kwance bama-bamai 56 a gadar da ke kan titin Marte zuwa Dikwa a jihar Borno.

Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce wannan nasara ta daƙile yunƙurin ƴan ta'adda na kai farmaki kan bayin Allah.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta'addan Boko Haram da ISWAP sun koma amfani da bama-bamai sakamakon matsin lambar da sojoji suke masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.