Sojojin Najeriya Sun Daƙile Mummunan Shirin Ƴan Ta'adda, An Gano Bama Bamai Sama da 50

Sojojin Najeriya Sun Daƙile Mummunan Shirin Ƴan Ta'adda, An Gano Bama Bamai Sama da 50

  • Sojoji da jami'an JTF sun gano tare da kwance bama-bamai 56 a gadar da ke kan titin Marte zuwa Dikwa a jihar Borno
  • A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce wannan nasara ta daƙile yunƙurin ƴan ta'adda na kai farmaki kan bayin Allah
  • Rahoto ya nuna cewa ƴan ta'addan Boko Haram da ISWAP sun koma amfani da bama-bamai sakamakon matsin lambar da sojoji suka masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Dakarun Rundunar Sojin Najeriya da ke aiki a ƙarƙashin Operation Hadin Kai tare da haɗin gwiwar Jami'an CJTF sun samu nasarar daƙile shirin ƴan ta'adda.

Dakarun sun gano tare da kwance bama-bamai 56 da aka birne a gadar da ke kan hanyar Marte zuwa Dikwa a jihar Borno.

Dakarun sojin Najeriya sun dakile shirin yan ta'adda.
Sojoji sun yi nasarar kwance bama-bamai 56 a jihar Borno Hoto: @NigeriaArmy
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojin ƙasan Najeriya ta wallafa a shafinta na X yau Juma'a, 4 ga watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Boko Haram/ISWAP suka dasa bama-bamai

Sanarwar ta ce ana kyautata zaton 'yan ta'addan Boko Haram ko ISWAP ne suka birne wadannan abubuwan fashewa domin kai hare-hare kan masu bin gadar.

Sojojin sun bayyana cewa tawagar masu kwance abubuwan fashewa (EOD) daga sansanonin soji na Marte da Dikwa ne suka jagoranci aikin tsaftace yankin daga barazanar bama-bamai.

“Ya zuwa yanzu, an samu nasarar ganowa tare da kwance bama-bamai 56 da aka binne su a wurin."
“Ana ci gaba da bincike ta hanyar amfani da fasaha domin gano sauran waɗanda aka binne da kuma kwance su gaba ɗaya domin tabbatar da tsaron yankin," in ji sanarwar.

Sojoji sun yi nasarar daƙile shirin ƴan ta'adda

Rundunar sojin ta kara da cewa wannan nasara ta ɗakile faruwar mummunan hare-haren da zai iya salwantar da rayuka da dukiyoyin masu ɗumbin yawa.

Ta jaddada cewa hakan na nuna irin gogewa, shiri, da jajircewa da sojojin Najeriya ke yi wajen kare muhimman ababen more rayuwa da rayukan jama'a a yankin Arewa maso Gabas.

An bayyana cewa yankin da aka gano wadannan bama-bamai na daga cikin wuraren da 'yan ISWAP suka kai hari a kwanakin baya.

Sojoji sun samu nasara a jihar Borno.
Dakarun sojojin Najeriya sun matsa wa ƴan ta'adda a Arewa maso Gabas Hoto: @NigeriaArmy
Asali: Twitter

Ƴan ta'adda sun canza salo a Borno

Saboda matsin lamba daga hare-haren soji, 'yan Boko Haram sun koma amfani da dabarar yaƙin sari-ka-noƙe, inda suke kai farmakim ba-zata da kuma amfani da bam a kan fararen hula da jami’an tsaro.

An ruwaito cewa akalla mutane 34 ne suka mutu sakamakon bam da 'yan ta'adda suka dasa tun farkon shekarar nan.

Jiragen soji sun yi wa ƴan bindiga lugude

A wani labarin, kun ji cewa jiragen rundunar sojin sama sun yi wa ƴan bindiga luguden wuta bayan kisan sojoji akalla 17 a jihar Neja.

Dakarun sashe na 1 na Operation Fansan Yamma sun kashe gomman ƴan bindiga a wani samame ta sama da suka kai domin agazawa sojojin kasa a jihar.

Jiragen yaƙin sojin saman sun kai hari ne kan ‘yan ta’addan da ke da hannu a hare-haren da suka faru a jihar Neja kwa nan nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262