Gwamnatin Najeriya za Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata 30,000

Gwamnatin Najeriya za Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata 30,000

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin ɗaukar ma’aikata 30,000 a hukumomin NSCDC, NIS da sauransu domin a inganta tsaro
  • Rahotanni sun nuna cewa za a fara tattara bayanan masu neman aikin daga ranar 26 ga Yuni ta shafi na musamman da aka tanada
  • An bayyana cewa dole ne masu neman aikin su zama ‘yan Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 da kuma sauran sharudan da aka kafa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin ɗaukar ma’aikata guda 30,000 a hukumomin tsaro guda huɗu na ƙasa, a wani mataki na cike gibin ma’aikata da ƙarfafa tsaron cikin gida.

Rahotanni sun bayyana cewa za a fara tattara sunayen masu neman aikin daga ranar 26 ga watan Yuni.

Gwamnatin Najeriya za ta dauki matasa 30,000 aiki
Gwamnatin Najeriya za ta dauki matasa 30,000 aiki. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta fitar, an bayyana cewa masu neman aikin za su ziyarci shafin yanar gizon nan domin tura bayanansu da zarar an bude shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daukar aikin zai shafi hukumar Kwastam ta Najeriya (NIS), Hukumar Gidajen Gyara Hali (NCoS), Hukumar kashe gobara ta Tarayya (FFS), da kuma Rundunar Tsaron Farin Kaya (NSCDC).

An bayyana sharudan daukar ma'aikata 30,000

A cewar sanarwar, dole ne wadanda za su nemi aikin su kasance ‘yan Najeriya, masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35, tare da samun cikakken lafiyar jiki da kwakwalwa.

Ma’aikata maza za su kasance masu tsawon jiki aƙalla 1.65m, tare da faɗin ƙirji bai gaza 0.87m ba, yayin da ake bukatar mata masu tsayin jiki aƙalla 1.60m.

Baya ga haka, dole ne duk wanda ke neman aikin ya kasance mutum mai halayya nagari, ba tare da wani tarihin laifi a baya ba.

Takardun da ake bukata don neman aikin

The Cable ta wallafa cewa an ce ana buƙatar takardar kammala makarantar sakandare (SSCE) tare da samun aƙalla darussa huɗu ko biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.

Haka kuma, masu takardu kamar NCE, OND, HND, da digiri a fannonin da suka shafi aikin, kamar fannin lafiya da kuma fasaha za su iya neman aikin.

An bayyana sharudan daukar matasa 30,000 aiki
Gwamnatin Najeriya ta bayyana sharudan daukar matasa 30,000 aiki. Hoto: NSCDC Nigeria
Asali: Twitter

Dole ne duk wanda zai nemi aikin ya zaɓi hukuma ɗaya kacal, domin kuwa ƙoƙarin neman fiye da ɗaya daga cikin hukumomin zai haifar da soke sunan mutum gaba ɗaya.

Za a rufe shafin neman aikin cikin mako 3

An bayyana cewa za a rufe shafin karɓar bayanan mutane bayan mako uku da bude shi, don haka aka bukaci masu sha’awar aiki da su gaggauta cikawa kafin ƙarewar wa’adin.

An shawarci ‘yan kasa da su bi ka’idojin da aka shimfiɗa domin guje wa soke sunayensu ko wata matsalar.

Legit ta tattauna da Adamu Ahmed

Wani matashi da ya kammala jami'ar jihar Gombe, Adamu Ahmed ya zantawa Legit cewa zai gwada sa'arsa wajen neman aikin.

Adamu Ahmed ya ce:

"Ina fata gwamnati za ta yi adalci wajen zaben mutanen da suka cancanta."

Dangote zai dauki matasan Najeriya aiki

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin Dangote ya bude kofa domin daukar matasan Najeriya aiki da ba su horo.

Kamfanin Dangote ya bayyana cewa hakan na cikin kokarin da ya ke kowace shekara domin tallafawa matasan Najeriya.

Matasan da suka kammala karatu a matakin digiri a jami'o'i ko HND a kwalejoji ne za su samu damar neman shiga cikin shirin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng