LEEP: An Kaddamar da Shirin Samawa Matasa Miliyan 2.5 Aiki a Najeriya

LEEP: An Kaddamar da Shirin Samawa Matasa Miliyan 2.5 Aiki a Najeriya

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kaddamar da shirin LEEP mai nufin samar da ayyuka miliyan 2.5 ga ‘yan Najeriya a fannoni daban-daban
  • Shirin da Ma’aikatar Kwadago ta tarayya ta tsara zai horar da matasa da basirar zamani da na kasuwanci don farfado da tattalin arzikin kasa
  • Kashim Shettima ya bukaci matasa su daina guduwa ƙasashen waje, maimakon haka su ci gaba da amfani da damar da ke akwai a cikin ƙasarsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kaddamar da shirin LEEP wanda ke da nufin samar da ayyukan yi miliyan 2.5 a fadin kasar nan.

An kaddamar da shirin ne a ranar Talata, 16 ga Afrilu, a Abuja, inda Shettima ya bayyana LEEP a matsayin wata babbar dama da gwamnatin Tinubu ta samar don yakar rashin aikin yi.

Kara karanta wannan

'Ka tsaya matsayinka': Gargadin da Shettima ya yi wa shugaban hukumar alhazai

Shirin LEEP
Shettima ya kaddamar da shirin samar da ayyuka wa matasa a Abuja. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kaddamar da shirin ne a cikin wani sako da Kashim Shettima ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

LEEP na cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin Tinubu karkashin kudirin "Renewed Hope", kuma yana kunshe da ginshiƙai shida da za su tallafa wa matasa da horo da kayan aikin zamani.

Bukatar sabunta sana'o'in hannu

Shettima ya bayyana cewa duniya na cikin wani sabon yanayi na canji, inda zamani ke kokarin kawar da ayyukan hannu, musamman na gargajiya.

Leadership ta wallafa cewa Kashim Shettima ya ce:

“Tsarin ayyuka na gargajiya yana shirin komawa tarihi, amma duk da haka, akwai dama mai yawa idan muka kasance masu lura wajen kokarin amfana da su."

Ya kara da cewa Najeriya na da yawan jama’a kuma tana amfani da harshen Ingilishi wanda zai ba ta damar zama cibiyar hada-hadar harkokin zamani.

Kira a zauna gida domin gina Najeriya

Shettima ya bukaci matasa da su daina barin kasa da nufin neman arziki a waje, yana mai cewa Najeriya na da isassun damammaki da za su iya ciyar da kowa gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta ba da hutun kwanaki 2 domin bukukuwan Kiristoci

“Muna da yawan jama’a fiye da miliyan 230, kuma nan da 2050, za mu kai miliyan 440. Wannan babbar dama ce da ya kamata mu amfana da ita maimakon guduwa zuwa ketare,”

- Kashim Shettima

Shettima
'Yan kwadago da ministoci yayin kaddamar da shirin LEEP a Abuja. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Maganar ministan kwadagon Najeriya

Ministan Kwadago, Maigari Dingyadi, ya bayyana cewa gwamnati na da cikakken shiri da niyya wajen samar da hanyoyin dogaro da kai da kuma yakar rashin aikin yi da dabaru masu dorewa.

Maigari Dingyadi ya ce:

“LEEP zai taimaka wajen gano hazaka, gina karfin matasa da hada su da masu bukatar aiki. Hakan zai karfafa zaman lafiya da kuma tattalin arzikin kasa."

Ya kara da cewa shirin zai shafi dukkan fannonin tattalin arziki, fasaha za ta kasance gadar sadarwa tsakanin masu aiki da masu neman aiki.

Legit ta tattauna da wani matashi

Wani matashi mai suna Yusuf Muhammad ya zantawa Legit cewa ya shafe shekaru kusan 4 bayan kammala karatu ba tare da ya samu aiki ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kafa sababbin dokoki a Filato saboda kashe kashe

"Idan har da gaske ne, za a rage matsalolin rashin aikin yi. Mutane miliyan 2.5 suna da yawa, muna fata mu shiga ciki.
"Kuma ya kamata gwamnati ta fitar tsare tsare da za su nuna da gaske take ba siyasa za a yi ba."

- Yusuf Muhammad

An raba babura don bunkasa noma a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta samar da babura 300 ga malaman gona domin shiga karkara.

An raba baburan ne a matsayin rance ba tare da kudin ruwa ba domin bunkasa noma da samar da abinci a jihar.

Malaman gona da suka samu shiga shirin sun bayyana cewa samun baburan zai taimaka musu wajen yin aiki yadda ya kamata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng