Sanata Ningi Ya Dauki Zafi, Yana Son Majalisa Ta Binciki Rashin Biyan Yan Kwangila Hakkokinsu

Sanata Ningi Ya Dauki Zafi, Yana Son Majalisa Ta Binciki Rashin Biyan Yan Kwangila Hakkokinsu

  • Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ahmed Ningi ya bukaci bincike kan dalilin da ya sa kudin yan kwangilar ayyukan gwamnati ya makale tun 2024
  • Ya bayyana takaicinsa ganin yadda aka kammala kusan 80% na ayyukan mazabu watanni shida da suka gabata, amma kudinsa shiru
  • Sanata Abdul Ningi ya ce wasu sun fara yada cewa ma’aikatar kudi da ofishin akanta na kasa da nuna son rai wajen biyan kudin ayyukan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaSanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ahmed Ningi, ya nemi a gudanar da cikakken bincike kan zargin hana yan kwangila hakkokiksu.

Ya ce ana zaton gwamnatin tarayya tana bin masu aikin kwangila kudin ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024.

Sanatan Borno ta Tsakiya, Abdul Ningi
Sanata Ningi na son a nemo inda kudin yan kwangila ya makale Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

A bidiyon da Imran Muhammad ya wallafa a shafin X, Sanatan ya ce ana zargin an hana yawancin ‘yan kwangilar ma’aikatun gwamnati da hukumomi hakkokinsu tun a watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta gayyaci manyan jami’an gwamnati

Daily Post ta ruwaito cewa ko a watan Mayu, majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso a kan batun.

Sauran wadanda aka gayyata sun hada da Ministan Kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun; da Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Atiku Bagudu.

Majalisar dattawan Najeriya
Sanata Ningi ya ce ana zargin Ofishin Akanta Janar da son kai Hoto: The Nigerian Senate
Asali: Facebook

Yayin zaman majalisar dattawa ranar Talata, Sanata Ningi ya musanta rade-radin da ke cewa gwamnati ba ta da kudin biyan ‘yan kwangilar.

Ya bayyana cewa babu wani dalili da zai za a rika buya a bayan Najeriya ba ta da kudi, wajen rike hakkokin yan kwangila da suka yi aiki kamar yadda aka amince su yi.

Ana son majalisa ta binciki bashin yan kwangila

Sanata Abdul Ahmed Ningi ya kuma bukaci majalisar dattawa ta umurci kwamitin kasafi da ya binciko ainihin dalilin da yasa ba a biya kudin ba.

A cewarsa:

“Yawancin ayyukan mazabu da na sani, 80% an kammala su tun fiye da watanni shida da suka gabata."
“Kuma yanzu ana ta yayata cewa ma’aikatar kudi da ofishin babban akanta na kasa suna zaben irin ayyukan da za su biya; wannan ba daidai ba ne."
“Ina ganin ya kamata a ba kwamitin kasafi wannan aiki. A umarce shi da ya kawo rahoto cikin makonni biyu kan dalilin da yasa wannan abu ke faruwa.”

Yana ganin kwamitin zai kawo masu cikakken bayani duka abin da ke wakana a kan batun makalewar kudin aikin yan kwangilar gwamnati.

Rigima ta barke a tsakanin yan majalisa

A wani labarin, mun wallafa cewa takaddama ta barke tsakanin 'yan majalisar wakilai biyu daga jihar Osun; Hon. Bamidele Salam da Hon. Oluwole Oke.

Lamarin ya biyo bayan rade-radin da ake na cewa jam’iyya mai mulki ta APC na kokarin jawo Gwamna Ademola Adeleke ya sauya sheka daga PDP kafin zaben 2026.

A cewar Bamidele Salam, wanda ke wakiltar mazabar Ede ta Kudu, Ede Arewa, Egbedore da Ejigbo, maganar cewa Gwamna Adeleke na shirin komawa APC karya ce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.