Gwamna Zai Dauki Malamai 4000 Aiki, Za Su Koyar da Yara a Firamare da Sakandare
- Gwamna Alex Otti ya ce za a dauki sababbin malamai 4,000 domin cike gibin da ake da shi a makarantun firamare da sakandare a fadin jihar Abia
- Ya bayyana cewa hakan na da nasaba da yawan ɗalibai da aka samu tun bayan kaddamar da tsarin ilimi kyauta da gwamnati ta ayyana tun watan Janairu
- Gwamnan ya ce baya ga gyaran makarantu da ɗaukar malamai, gwamnati na shirin kammala gyaran asibitocin matakin farko guda 200 a fadin jihar Abia
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - Gwamnan Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa za a ɗauki malamai 4,000 aiki domin ƙara yawan sababbin malamai a makarantun firamare da sakandare na jihar zuwa 9,394.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawa da kafofin watsa labarai na wata-wata, wanda aka gudanar a daren Alhamis a gidan gwamnati da ke Umuahia.

Asali: Twitter
Gwamna Otti zai dauki malamai 4,000 aiki
Alex Otti ya ce za a tura rukunin farko na malamai 5,394 da aka riga aka ɗauka aiki bayan kammala horon su a Aba da Umuahia, a cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar gwamnan, za a fara ɗaukar sababbin malaman da zarar an kammala horon, yana mai cewa, "Za mu buɗe shafin yanar gizo don ba masu sha'awar aikin su nema."
Alex Otti ya ce manufar ita ce a samar da isassun malamai a makarantun jihar, ganin yawan ɗaliban da aka samu tun bayan aiwatar da tsarin ilimi kyauta.
Hukumar dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatin jihar ta ayyana tsarin ba da ilimin firamare da sakandare kyauta da kuma tilasta shi a watan Janairu.
Gwamnan jihar Abia ya ayyana ilimi kyauta
Gwamnatin Alex Otti ta ce ta bullo da tsarin don tabbatar da cewa kowane yaro a Abia, yana da damar samun ilimi har zuwa sakandare ba tare da kashe ko sisi ba.
Otti ya jaddada buƙatar samar da ingantattun malamai ga makarantun firamare da sakandare a faɗin jihar.
Ya bayyana jajircewar gwamnatinsa wajen gyara makarantu, yana mai cewa:
"Bayan gyare-gyaren makarantun, mun kuma daga darajar wasu makarantu 20 zuwa makarantun zamani, yayin da muke kan aikin wasu."

Asali: Facebook
Alex Otti ya inganta kiwon lafiya a Abia
Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a kammala gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 200 a faɗin ƙananan hukumomi 17 na jihar.
"Tuni muka kawo kayayyakin aikin da kuke kallonsu a ƙasashen da suka ci gaba kuna jin dadi, kuma za mu tabbatar mun wadata cibiyoyin kiwon lafiya da irin kayayyakin nan a Abia."
- Gwamna Alex Otti.
Otti, wanda ya fito da wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a sauran fannoni, ciki har da tsaro, hanyoyi, tsaftar muhalli da sauransu, ya yi kira ga mazauna jihar da su haɗa hannu da gwamnati wajen gina sabuwar Abia.
Otti zai yi ritaya bayan barin Gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa jita-jitar cewa zai tsaya takarar kujerar sanata bayan mulkinsa karya ce babu tushe balle makama.
Otti ya nesanta kansa daga rade-radin da ke yawo, yana mai jaddada cewa zai yi ritaya daga siyasa ne gaba daya idan ya kammala wa'adinsa na gwamna.
Alex Otti ya bayyana bukatar ba matasa damar shugabanci saboda yadda al'umma ke sauyawa tare da karuwar fitowar matasa domin kawo sauyi mai ma'ana a jiha da kasa baki daya.
Asali: Legit.ng