Dangote Ya Fara Daukan Matasan Najeriya Aiki domin ba Su Horo

Dangote Ya Fara Daukan Matasan Najeriya Aiki domin ba Su Horo

  • Kamfanin Dangote ya buɗe ƙofar shirin horas da matasa ‘yan Najeriya da suka kammala digiri ko HND da ke neman ƙwarewar aiki
  • Ana buƙatar masu neman guraben su kasance ‘yan kasa da shekara 28 da haihuwa kuma su mallaki shaidar hidimar kasa ta NYSC
  • An bayyana cewa shirin zai bai wa matasa dama su ƙara ƙwarewa, gina kwarin gwiwa da ƙarfafa matsayinsu a harkokin sana’a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin Dangote ya sanar da buɗe damar shiga shirin horar da matasa ‘yan Najeriya da suka kammala karatun jami’a ko HND.

Shirin dama ce ga sababbin masu digiri ko babbar difloma ta HND da ke neman samun ƙwarewa da gogewa a fannin aiki.

Dangote
Dangote ya fitar da sharudan daukan matasan Najeriya aiki domin ba su horo. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Legit ta tattaro bayanai kan shirin ne a wani sako da kamfanin Dangote ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin na 2025 ya ƙunshi horo na musamman da zai taimaka wajen haɓaka ƙwarewa da gina kwarewar aiki cikin yanayi na hadin gwiwa da koyo daga kwararru.

Sharudan daukar matasa a kamfanin Dangote

Daga cikin sharuddan shiga shirin akwai kasancewa dan shekaru 28 ko ƙasa da hakan a lokacin neman gurbin aikin.

Haka kuma, dole ne mutum ya mallaki kwalin digiri da mafi ƙarancin darajarsa ta kai Second Class Lower daga jami’a ko Upper Credit daga HND.

Kamfanin ya kuma bayyana cewa dole ne mai neman gurbin ya gabatar da takardar shaidar kammala NYSC ko takardar sallama daga wadanda ba su yi hidimar ba.

Yadda za a nemi aiki a kamfanin Dangote

Duk wanda ya cika sharudan da aka ayyana kuma yana sha'awar neman aikin zai ziyarci shafin yanar gizon kamfanin a nan domin tura bayanai.

Ana sa ran kamfanin Dangote zai tuntubi dukkan wadanda suka cancanta bayan tantancewa domin fara aiki da su.

Dangote na gina rayuwar miliyoyi mutane

A cewar kamfanin, babban burinsu shi ne tallafa wa mutane ta hanyar samar da kayayyakin bukatun a yau da kullum da kuma raya kasashe musamman a yankin Afrika.

A karkashin haka ne suke samar da shirye shirye irin wannan domin ba matasa damar kwarewa wajen koyo da gina sana'a.

Ayyuka da tsare-tsaren kamfanin Dangote

Kamfanin Dangote yana da tsari na musamman na inganta rayuwar mutane ta hanyar samar da kayan abinci da sauran kayayyakin more rayuwa.

Ayyukansa da tsare-tsarensa sun samo asali ne daga hangen nesa na kafa kamfanoni daban daban da za su rika biyan bukatun al’umma na yau da kullum.

Dangote
Dangote zai ba matasan Najeriya horo. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Tarihin da cigaban kamfanin Dangote

Dangote ya fara ne da kasuwancin sayar da kaya tun a 1970, lokacin da tsarin shigo da kaya daga waje ya samu karbuwa wajen gwamnatin Najeriya.

Daga bisani kamfanin ya mayar da hankali kan samar da kaya a gida don rage dogaro da kayayyakin waje.

Dangote zai kafa kamfanin sukari a Ghana

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote zai kafa katafaren kamfanin sukari a kasar Ghana.

Ana sa ran kamfanin zai samar da ayyuka ga dimbin mutane, musamman matasan da ba su da aikin yi.

Baya ga samar da ayyuka, Dangote ya bayyana cewa kamfanin sukarin zai habaka tattalin kasashen Afrika ta Yamma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng