'Yan Bindiga Sun Budewa Matafiya Wuta a kan Hanya, an Samu Asarar Rai
- Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan wasu matafiya a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya
- Miyagun ƴan bindigan sun farmaki matafiyan ne lokacin da suke kan titin hanyar Anka-Mayanchi a ƙaramar hukumar Talata Mafara
- Harin da ƴan bindigan suka kai kan matafiyan ya jawo an samu asarar ran ɗaya daga cikin fasinjojin da ke cikin motar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan matafiya a ranar Laraba a kan titin Anka-Mayanchi da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a kihar Zamfara.
A yayin harin, ƴan bindigan sun kashe mutum ɗaya, suka jikkata wasu biyu, sannan suka sace mutum ɗaya.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun farmaki matafiya a Zamfara
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne tsakanin ƙauyukan Bobo da Yashar Rogo, lokacin da ƴan bindigan suka tare motoci biyu ƙirar Golf da ke ɗauke da fasinjoji.
Ganau sun bayyana cewa ƴan bindigan sun buɗe wuta kai tsaye kan motocin, inda suka kashe mutum ɗaya nan take, suka jikkata wasu biyu, sannan suka sace wani fasinja ɗaya.
Mazauna yankin da kuma ƴan banga sun kawo ɗauki cikin gaggawa, inda suka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin jinya, sannan suka ɗauki gawar mamacin domin a yi masa jana’iza.
Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da ƙoƙarin ceto mutumin da aka sace.
Ƴan bindiga na yawan kai hare-hare a Zamfara
Wannan hanya da ke haɗa garuruwan Anka da Mayanchi ta fuskanci hare-hare da dama a ƴan watannin nan da suka gabata.
Ana dai zargin ƴan bindigan da ke ɓuya a dazukan yankin ne ke aikata irin waɗannan ta’addanci.

Asali: Original
A wani lamari makamancin haka, an sace wani likita mai suna Alhaji Abdullahi Dangulbi wanda ke aiki a asibitin gwamnati na Anka a ranar 21 ga watan Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe.
An ɗauke shi ne a ƙauyen Tashar Kalgo, kusa da garin Jangebe a ƙaramar hukumar Talata Mafara, yayin da yake tafiya daga Anka zuwa Gusau.
Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga
- 'Yan bindiga sun addabi mutane da hare hare a Kogi, an sake yin barna
- DSS ta sake cafke wani riƙakken dan bindiga da ke ƙoƙarin tafiya aikin Hajji a Sokoto
- Sojoji sun kashe babban abokin Bello Turji bayan luguden wuta suna shirya taro
Ƴan bindiga sun farmaki manoma
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindigan sun kai hari kan manoman da ke aiki a gonakinsu a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun farmaki manoman ne a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kankara inda suka hallaka guda uku daga cikinsu lokacin da suke aikin sharar gona.
Dakarun sojoji da sauran jami'an tsaro sun kai ɗaukin gaggawa, sai dai kafin su isa zuwa wajen, ƴan bindigan sun ranta a na kare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng