Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Ranar da Tinubu Ya Je Kaduna

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Ranar da Tinubu Ya Je Kaduna

  • Akalla mutane 15 ne suka mutu a hare-haren da aka kai Bokkos da Mangu a jihar Filato, lamarin da ya jefa mutane cikin firgici
  • Rahotanni sun ce maharan sun yi ruwan wuta cikin dare a Tangur da Manja, inda suka kutsa cikin gidaje suka kashe mutane
  • 'Yan bindigar sun kai wadannan hare-hare ne a ranar da Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci Kaduna domin kaddamar da ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Akalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu a daren Alhamis, 19 ga Yuni, 2025, yayin da 'yan bindiga suka kai mummunan hari a Bokkos da Mangu na jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai farmaki kauyen Manja da ke Chakfem a Mangu, da kuma kauyen Tangur a Bokkos, lamarin da ya jefa mazauna yankunan cikin firgici.

'Yan bindiga sun kutsa har cikin gidaje, sun kashe mutane 15 a Filato
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, yayin da yake alhinin halin da ake ciki a jihar. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

'Yan bindiga sun kashe mutum 15 a Filato

Wani rahoton Daily Trust ya ce 'yan bindigar sun shiga kauyen Tangur da misalin ƙarfe 9:00 na dare lokacin da mutane ke shirin kwanciya, yayin da harin Chakfem ya faru tun da rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun yi ruwan wuta ba kakkautawa tare da kutsa wa cikin gidaje suna kashe mutane.

A Mangu, mutane bakwai aka kashe, yayin da a Bokkos kuwa aka hallaka takwas, lamarin da ya jefa mutanen wadannan garuruwa cikin tsananin alhini.

An tabbatar da hare-haren 'yan bindiga a Filato

Shugaban kungiyar cigaban Mwaghavul kuma daraktan sansanin 'yan gudun hijira na Mangu, Shohotden Mathias Ibrahim, ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu a Mangu.

Kokarin da aka yi don jin ta bakin shugabannin al’umma a Bokkos ya ci tura, haka kuma kakakin rundunar ‘yan sandan Filato, DSP Alfred Alabo, bai mayar da martanin sakonnin da aka aika masa ba har zuwa safiyar Juma’a.

Hare-haren na ci gaba da zama ruwan dare a jihar Filato, inda akasari ake danganta su da rikicin manoma da makiyaya kan filayen noma da albarkatu.

Rahoton Amnesty International ya nuna cewa mutane 2,630 ne suka mutu a Filato cikin shekaru biyu, yayin da aka tilasta wa 65,000 barin gidajensu.
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang yayin da yake rarrashin daya daga cikin wadanda hare-haren 'yan bindiga ya rutsa da su. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

An kashe mutum 2,630 a Filato - Amnesty

Tun farkon 2025, hare-haren da suka afku a Bokkos sun yi sanadin mutuwar mutum 52 tare da tilasta wa fiye da 2,000 kauracewa gidajensu.

Rahoton Amnesty International ya nuna cewa mutane 2,630 ne suka mutu a jihar cikin shekaru biyu, yayin da aka tilasta wa 65,000 barin muhallansu.

Ko da yake babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kisan na baya-bayan nan, amma galibi ana alakanta irin wadannan hare-haren da Fulani makiyaya.

Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara a jihar Kaduna domin ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan cigaba.

A ziyarar da kai Kaduna a ranar Alhamis, 19 ga Yuni, Shugaba Tinubu ya kaddamar da asibitin kwararru mai gado 300 da kuma cibiyar koyon sana’o’i da ke Rigachikun.

A wajen taron kaddamar da ayyukan ne, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya shaida wa Tinubu cewa ba shi da wani abokin hamayya a Kaduna

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.