'Yar Isra'ila Ta Rasa Ranta sanadin Bugun Zuciya a Harin Makami Mai Linzami daga Iran

'Yar Isra'ila Ta Rasa Ranta sanadin Bugun Zuciya a Harin Makami Mai Linzami daga Iran

  • Wata mata mai shekara 51 ta rasu sakamakon bugun zuciya yayin da take buya daga harin makami a Karmiel da ne birnin Haifa
  • Hukumar agaji a Isra'ila ta ce mutane 23 sun jikkata a Haifa, ciki har da yaro dan shekara 16 da wasu maza biyu sun samu rauni a kafa
  • Sojoji sun ce Iran ta harba makamai 25, babu rahoton rauni a yankin Tsakiyar da Kudancin Isra’ila a harin na baya-bayan nan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Haifa, Isra'ila - Kasar Iran ta sake kai wani mummunan hari cikin birnin Haifa da ke Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wata mata mai shekaru 51 ta fadi ta mutu bayan da ta kamu da bugun zuciya yayin da take buya domin tsira da rayuwarta.

Harin Iran ya yi ajalin mutane a Isra'ila
Iran ta sake harba makami mai linzami a Isra'ila. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

The Times of Israel ta tabbatar da cewa matar ta mutu ne a garin Karmiel da ke Arewacin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hare-hare Iran a Isra'ila ya jikkata al'ummomi

Hakan ya biyo bayan cigaba da hare-haren da ake kai wa juna tsakanin Iran da Isra'ila wanda aka shafe kwana takwas ana yi.

Rahotanni sun ce yakin ya daidaita al'ummomi da jawo asarar rayuka da dukiyoyi tare da gaba mutane da muhallansu.

Hakan ya tilasta wasu daga cikin Yahudawa yan Isra'ila barin gidajensu da karfi da yaji saboda hare-hare daga Iran.

Yadda Iran ta yiwa Isra'ila barna a yau

Harin na yau ya faru ne yayin da kararrawa ke gargadin wani sabon harin makamai daga Iran.

Hukumar agajin gaggawa ta Magen David Adom (MDA) ta ce an bayyana mutuwar matan bayan an yi kokarin ceto rayuwarta amma hakan bai yiwu ba.

Hukumar ta kara da cewa adadin wadanda suka jikkata sakamakon harin da ya shafi Haifa ya kai mutane 23.

A cewar MDA, uku daga cikinsu sun samu munanan raunuka yayin da wani yaro dan shekara 16 da ya samu rauni saboda fashewar gurneti.

Iran ta sake kai farmaki Isra'ila a yau Juma'a
Harin makami mai linzami ya illata kasar Isra'ila. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Yawan mutanen da suka jikkata a Isra'ila

Har ila yau, wasu maza biyu, daya mai shekara 54 da daya mai shekara 40 da suka jikkata a kafafu, cewar The Jerusalem Post.

Mutane 20 daga cikin wadanda suka jikkata a Haifa sun samu raunuka da ake ganin da sauki amma lamarin ya rikita mazauna yankin.

Sojoji sun ce Iran ta harba makamai kimanin 25 a harin na baya-bayan nan, ba a samu rahoton rauni ba daga yankunan Tsakiyar da Kudancin Isra’ila.

Iran ta harba manyan makamai masu hatsari

Kun ji cewa Iran ta sake harba makamai masu linzami zuwa kasar Isra'ila a yau Juma'a, 20 ga watan Yuni, 2025 yayin da rikici ke ƙara ƙamari.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Isra'ila watau MDA ta ce akalla mutane biyu sun jikkata a sababbin hare-haren da Iran ta kai kan abokiyar gabanta.

Rundunar soji ta yi iƙirarin cewa ta harbo wasu daga cikin jirage marasa matuƙa da Iran ta cillo, amma duk da haka wasu sun sauka a kan gine-gine.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.