Mangu: An Kashe Bayin Allah 91 Yayin da Wasu 158 Suka Ji Raunuka a Rikicin da Ya Ɓarke a Jihar Arewa

Mangu: An Kashe Bayin Allah 91 Yayin da Wasu 158 Suka Ji Raunuka a Rikicin da Ya Ɓarke a Jihar Arewa

  • Shugaban matasan Mwaghavul ya bayyana adadin rayuka da dukiyoyin da aka rasa a rikicin da ya ɓarke a Mangu, jihar Filato makon jiya
  • Kwamared Sunday Ɗankaka ya ce mutane 91 sun mutu, wasu 158 sun ji raunuka yayin da aka ƙona gidaje da wuraren ibada
  • Rahoto ya nuna cewa rikicin ya faru ne duk da dokar zaman gida da Gwamnatin Filato ta sanya a karamar hukumar Mangu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Filato - Shugaban kungiyar matasan Mwaghavul na kasa, Kwamared Sunday Dankaka, ya ce mutane 91 ne suka mutu a rikicin da ya barke a karamar hukumar Mangu a makon jiya.

Kwamared Ɗankaka ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Jos, babban birnin jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fusata, ya sanya dokar kulle a garuruwa biyu bayan faɗa ya kaure

Gwamna Celeb Mutfwang na jihar Filato.
Rikicin Filato: Mutane 98 Sun Mutu Yayin da Wasu 158 Suka Jikkata a Mangu Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Ya ce waɗanda rikicin Mangu ya yi sanadin mutuwarsu a makon jiya sun kunshi mata 42, ƙananan yara 37, da magidanta maza 12.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, mutane 158 ne suka samu raunuka a rikicin yayin da gidaje 114 suka kone, sannan kuma lamarin ya shafi masallatai 9 da coci-coci 15.

Rikicin ya afku ne ranar 22 ga watan Janairu, 2024 bayan wasu tsageru sun farmaki wani ɗan acaɓa, Ebenezer Caleb da karfe 5:45 na yamma wanda ya saɓa dokar zaman gida da gwamnati ta sanya.

Asalin abinda ya haddasa rikici a Mangu

Da yake bada labarin asalin abinda ya haddasa rikicin Mangu, Ɗankaka ya ce:

"Ɗan acaban ya ɗauko fasinja, Madam Jenifer Fidelis, suna hanyar zuwa gida Sabon Gari, suka tsaya domin baiwa shanun wasu makiyaya dama su tsallaka titi mita 50 kacal tsakaninsu da shingen bincike.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka shugabannin matasa 2 a jihar PDP

"Bayan shanun sun gama wucewa sai wani yaro makiyayi ya masa barazanar kisa saboda wai su (Mwagavul) sun hana su kiyo a yankunansu, nan fa yaron ya dake shi da sanda, sauran suka far masa.
"A wannan lokacin sojoji ba su ce komai ba, daga baya suka ce ai shi ɗan acaban ne ya tono faɗan. Wannan ne ya fusata matasa saboda babu wani mataki da aka ɗauka."

A halin yanzu ana ta kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kai kayan agaji ga waɗanda wannan faɗa ya shafa a kananan hukumomin Bokkos da Mangu, rahoton Daily Post.

Mahara sun halaka shugabannin matasa 2

A wani rahoton kuma Wasu mutane ɗauke da bindigu sun halaka shugabannin matasa biyu kisan gilla a jihar Delta ranar Litinin.

Tsohon sanata a jihar, Chief Ighoyota Amori, ya yi tir da wannan kisan, inda ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da sauran al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel