Bayan Radawa Asibiti Sunan Tinubu a Kaduna, Shugaban Kasa Ya Yi wa Jihar Alkawari

Bayan Radawa Asibiti Sunan Tinubu a Kaduna, Shugaban Kasa Ya Yi wa Jihar Alkawari

  • Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya sanya wa sabon asibiti na musamman da aka kammala suna Bola Ahmed Tinubu, domin karrama shugaban kasa
  • Rahotanni sun nuna cewa asibitin yana da sassa guda tara da suka hada da kula da matan da suka haihu da jariransu da sashen ba da kulawar gaggawa
  • Gwamnan ya bukaci tallafin shugaban kasa wajen kammala gina cibiyar kula da cutar daji, wanda hukumar kula da makamashin nukiliya ta amince da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - A yayin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki zuwa Kaduna domin kaddamar da ayyuka, an radawa asibiti sunan shi.

Gwamna Uba Sani ne ya radawa sabon asibitin da aka gina a jihar sunan Mai girma Bola Ahmed Tinubu Specialist Hospital.

An sanya wa asibiti sunan Bola Tinubu a Kaduna
An sanya wa asibiti sunan Bola Tinubu a Kaduna. Hoto: @YP4Tinubu
Asali: Twitter

A wani sako da fadar shugaban kasa ta wallafa a X a ranar Alhamis, ta tabbatar da sanyawa asibitin sunan Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa hakan wani yunkuri ne na girmamawa ga shugaban kasa bisa irin jagorancin sa da jajircewarsa wajen tabbatar da ci gaban Najeriya.

Gwamnan Kaduna ya nemi taimako kan cutar daji

Yayin da yake jawabi a wurin bikin bude asibitin, Uba Sani ya ce hukumar kula da makamashin nukiliya ta amince da kafa cibiyar kula da cutar daji da na’urorin nukiliya a cikin asibitin.

Sai dai ya bayyana cewa akwai bukatar karin tallafi domin kammala wannan bangare mai matukar amfani ga lafiyar jama’a.

Rahoton Arise News ya nuna cewa Uba Sani ya ce:

“A halin yanzu, wannan ne kawai sashen da ba a kammala ba. Muna neman taimakon shugaban kasa domin cika wannan bangare mai muhimmanci,”

Tinubu ya amsa bukatar Uba Sani a Kaduna

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da namijin kokarin Gwamna Uba Sani, inda ya ce aikin da gwamnan ke yi ya nuna cewa yana da hangen nesa da kulawa da jin dadin al’ummarsa.

Shugaba Tinubu ya ce:

“Ina matukar alfahari da abin da kake yi.
"Mun ga ci gaba, kuma ka fifita bukatun jama’a. Shugaba mai hangen nesa ne kaɗai zai iya gina irin wannan asibiti don kula da lafiyar al’umma,”

Shugaban kasar ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa wajen ganin an kammala cibiyar kula da cutar daji da ke cikin wannan asibiti na musamman.

Shugaba Tinubu tare da Uba Sani
Shugaba Tinubu tare da Uba Sani a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Shugabanni sun tarbi Bola Tinubu a Kaduna

Tinubu ya isa Kaduna cikin tarba mai armashi daga shugabanni da dama, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin.

Haka zalika, Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya kasance cikin wadanda suka tarbi shugaban kasar.

Gwamna Hope Uzodimma na Imo, Babajide Sanwo-Olu na Legas, Biodun Oyebanji na Ekiti, Monday Okpebholo na Edo, Umar Namadi na Jigawa sun halarci bikin.

SDP ta ce za ta kayar da Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar SDP mai adawa a Najeriya ta ce tana da tabbacin kayar da Bola Tinubu a 2027.

Shugaban jam'iyyar na jihar Ebonyi ne ya bayyana haka yana mai cewa za su kayar da Bola Tinubu kamar yadda aka yi wa Goodluck Jonathan.

Jam'iyyar SDP ta ce akwai dabarun da ta ke yi a boye wajen ganin ta samu nasara, kuma mutane za su sha mamaki kan yadda za ta tunkari siyasar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng