Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Shammaci Mutane da Dare, Sun Dauke Liman da Mutum 5
- ‘Yan bindiga sun sace limamin Fangaltama da wasu mutum biyar a wani sabon hari da suka kai a Talata Mafara da ke jihar Zamfara
- Harin ya auku ne da misalin karfe 3:00 na asubahin ranar Laraba kusa da sansanin soja, inda suka harbi wata mata mai suna Basira Abdullahi
- Rundunar tsaro ta isa yankin, amma ‘yan bindigar sun tsere da wadanda suka sace kafin isowar jami’an tsaro wanda hakan ya sake firgita al'umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Al'ummar wasu yankuna a jihar Zamfara sun wayi gari da mummunan labari bayan harin yan bindiga a yankin.
An ce wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a kauyen Fangaltama da ke yankin Talata Mafara a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

Asali: Twitter
Yan bindiga sun harbe wata mata a Zamfara
Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa harin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na asuba a ranar Laraba 18 ga watan Yunin 2025 a muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa harin ya faru ne lokacin da miyagun suka dira kauyen da ke kusa da sansanin soja.
Sun bude wuta babu kakkautawa, wanda ya haifar da firgici da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa a lokacin harin, wata mata mai suna Basira Abdullahi ta gamu da tsautsayi na harbin bindiga.
Yadda aka sace limamin masallaci a Zamfara
Bayan kaddamar da harin, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutane shida ciki har da limamin kauyen, Liman Hamisu Ali.
Wadanda aka sace dukkansu ‘yan kauyen ne, kuma har yanzu ba a san inda suka nufa da su ba.
Rundunar tsaro ta yi gaggawar kai dauki zuwa yankin domin fuskantar ‘yan bindigar da kuma ceto mutanen.
Sai dai zuwa lokacin da jami’an tsaro suka isa kauyen, ‘yan bindigar sun riga sun tsere da wadanda suka sace.

Asali: Original
Rokon da mazauna yankin suka yiwa hukumomi
Lamarin ya sake tayar da hankali a jihar Zamfara da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da sace-sacen mutane.
Wannan lamari ya faru ne kusa da hanyar Gusau zuwa Sokoto, inda ake fama da kai hare-hare a baya-bayan nan.
Mazauna yankin sun roki gwamnati da hukumomin tsaro da su kara tsaurara matakai domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano inda aka kai wadanda aka sace.
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace limamin Juma'a
A baya, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun sace babban limamin masallacin Juma’a na Faru, Imam Sulaiman Idris da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kama limamin ne da safiyar Laraba yayin da yake aiki a gonarsa, kuma har yanzu ba a san inda yake ba.
Wani rahoto ya nuna cewa mazauna garin sun bayyana fargaba da fushi, suna kira ga hukumomin tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng