An Shiga Tashin Hankali a Filato, 'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Mai Uwa da Wabi

An Shiga Tashin Hankali a Filato, 'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Mai Uwa da Wabi

  • Masu garkuwa da mutane sun kashe mutum ɗaya tare da sace huɗu a wani mummunan hari a Shendai, Quaanpan da ke jihar Filato
  • Shugaban ƙaramar hukumar Quaanpan, Manship, ya tabbatar da lamarin tare da yin kira ga jami’an tsaro su gaggauta ceto mutanen
  • Manship ya ziyarci yankin tare da jami’an tsaro don tantance halin da ake ciki da kuma jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - An kai mummunan hari a Shendai da ke Quaanpan, jihar Filato, inda masu garkuwa suka kashe mutum ɗaya tare da sace wasu huɗu.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne a ranar Asabar, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tsoro da tashin hankali.

Shugaban karamar hukuma a Filato ya yi magana da yan bindiga suka farmaki mutanensa
'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar Filato, an kashe mutum 1 da sace wasu hudu. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Filato

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya fara gyara hanyar Saminaka da ta hada jihohin Arewa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa masu garkuwar sun kai harin ne a gidan mutanen da suka sace, inda suka harbe mutum ɗaya suka kuma tafi da wasu huɗu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙaramar hukumar Quaanpan, Christopher Audu Manship, ya tabbatar da harin cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Danaan Sylvanus, ya fitar.

Manship ya nuna damuwa kan ƙaruwar hare-hare da sace-sacen mutane a yankin, yana kira da a gaggauta ceto waɗanda aka sace.

Ciyaman ya ziyarci garin da aka farmaka

A sanarwar, Manship ya yi ta’aziyya ga al’ummar Shendai a Namu bisa mutuwar mutum ɗaya, tare da kira ga jami’an tsaro su ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro don tabbatar da tsaron kowa, tare da neman a ceto waɗanda aka sace.

Punch ta rahoto cewa shugaban ya ziyarci yankin da abin ya shafa tare da jami’an tsaro, ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanal Ogunrinde Soji.

Kara karanta wannan

"Zargin baki biyu": Fusatattun mutane sun bankawa gidan basarake wuta a Kano

'Yan bindiga sun farmaki kauyen Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mutane biyar sun rasa rayukansu a harin da wasu 'yan ta'adda suka kai kauyen Lighitlubang, ƙaramar hukumar Mangu, jihar Filato.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun kai harin da tsakar dare, lokacin da mazauna kauyen ke barci, suka hallaka wasu ta hanyar yankan rago.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.