El Rufa'i: A Karon Farko, Shugaba Tinubu Ya Caccaki Tsohuwar Gwamnatin Kaduna
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana gwamnatin da ta gabata a Jihar Kaduna a matsayin mai danniya da rashin tausayin jama’a
- Tinubu ya jinjina wa Gwamna Uba Sani bisa irin sauyin da ya kawo a Kaduna, yana cewa jihar na samun ci gaba da zaman lafiya
- Shugaban ƙasar ya ce an samu gagarumin sauyi a harkar tsaro tun bayan ziyararsa ta baya a 2022, musamman a yankin Birnin Gwari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna– Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, a matsayin ta danniya da rashin tausayin jama'a.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin kaddamar da Cibiyar Horar da Sana’o’i da Ƙwarewa a Rigachikun da kuma asibiti mai gadaje 300 a Millennium City, duk a Jihar Kaduna.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa shugaban ƙasar ya yabawa gwamnonin jam’iyyar APC bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bashi a tafiyar da mulkin ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya ce Kaduna ta ci gaba
Daily Post ta wallafa cewa Tinubu ya jinjina wa Gwamna Uba Sani bisa irin canjin da ya kawo a jihar Kaduna tun bayan hawansa mulki.
Ya ce gwamnan ya kubutar da jihar daga mulkin danniya da gwamnatin baya ta yi, yana mai bayyana sabuwar Kaduna a matsayin wadda ke samun ci gaba.

Asali: Facebook
A cewarsa:
“Uba Sani ya yi abin al’ajabi. Ya canja yanayin Kaduna daga danniya da rashin kwanciyar hankali zuwa jihar da ke bunkasa.”
“Kai shugaba ne nagari, kuma ina matuƙar farin cikin aiki da kai. Ina ganin na yi sa’a da samun ku a matsayin gwamna.”
Tinubu ya ga bambanci a jihar Kaduna
Shugaban ƙasar ya tuna da matsalolin tsaro da suka dabaibaye jihar a ziyararsa ta baya a shekarar 2022, yana mai bayyana cewa an samu babbar nasara a fannin tsaro tun daga lokacin.
Ya ce:
“Ina matuƙar jin daɗin zaman lafiya da ke gudana yanzu a Kaduna. Wannan ya bambanta ƙwarai da irin matsin lamba da tashin hankali da na tarar da su a ziyara ta ta baya a 2022.”
“Don kai wa gundumar Birnin Gwari yakin neman zaɓe a lokacin, sai da muka kusan tura dakarun runduna baki ɗaya (saboda rashin tsaro).”
Tinubu ya ƙara da cewa ya samu tabbaci daga hukumomi cewa an samu dawowar zaman lafiya a yankin da wasu sassan jihar Kaduna.
Shugaba Tinubu ya ziyarci jihar Kaduna
A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki zuwa Kaduna a ranar Alhamis domin kaddamar da muhimman ayyuka, ciki har da asibitin gadaje 300 da aka gina a Millennium City.
A yayin wannan ziyara, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa an radawa sabon asibitin suna Bola Ahmed Tinubu Specialist Hospital a matsayin wata hanya ta girmamawa ga shugaban ƙasa.
A yayin da yake jawabi a wajen bikin bude asibitin, Gwamna Uba Sani ya ce hukumar kula da makamashin nukiliya ta amince da kafa cibiyar kula da cutar daji da na’urorin nukiliya a cikin asibitin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng