Bayan Ziyarar Tinubu, Shugaban Majalisa Ya Fadi Inda Kuri'un Kaduna za Su Tafi a 2027
- Shugaban majalisar wakilan Najeriya ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan ayyukan da ya yi a jihar Kaduna
- Tajudeen Abbas ya bayyana cewa mutanen jihar Kaduna za su rama biki ga shugaban ƙasan a zaɓen 2027
- Shugaban majalisar wakilan ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar da muhimman ayyuka don ci gaban jihar Kaduna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ƙwararo yabo ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Tajudeen Abbas ya bayyana cewa mutanen jihar Kaduna ba su da wani zaɓi face Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027..

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban majalisar wakilan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Musa Krishi, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar da ayyuka masu muhimmanci a jihar Kaduna.
Tinubu zai samu ƙuri'u a Kaduna
Saboda wannan da wasu dalilai masu nasaba da hakan, Tajudeen ya ce mutanen jihar Kaduna sun shirya su ninka yawan ƙuri’un da Shugaba Tinubu ya samu a jihar a zaɓen 2023 a zaɓen 2027 mai zuwa.
“Kaduna ba ta da wata hujjar zaɓar wani daban a shekarar 2027. Na yi amanna da hakan ne saboda irin yadda gwamnatinka ke nuna ƙauna da aiki a zahiri ga jihar Kaduna."
"Ka ƙaddamar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa masu amfani kai tsaye ga jihar."
"Mai girma shugaban ƙasa, Kaduna tun da dadewa ta kasance cibiyar ƙasa ta fuskar siyasa, tattalin arziki da tarihi."
“A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, jam’iyyar APC ta samu kusan kaso 30% cikin 100% na ƙuri’un da aka kaɗa a jihar. Duk da cewa wannan sakamakon ya yi tasiri, har yanzu akwai damar ƙara wa."
"Saboda haka, a madadin gwamnanmu, jam’iyyarmu da al’ummarmu, ina tabbatar maka da cewa Kaduna ta ƙudiri aniyar yin fiye da hakan."
"Burinmu shi ne mu ninka wannan kaso da kuma tabbatar da samun aƙalla kaso 60% cikin 100% na ƙuri’u a shekarar 2027."
"Wannan ba kawai buri ne na siyasa ba, aiki ne da aka tsara tare da samun haɗin kan al’ummar da ta yadda da jagorancinka."
- Tajudeen Abbas

Asali: Twitter
Shugaban majalisa ya yabawa Tinubu
Haka zalika, shugaban majalisar wakilan ya yaba wa shugaban ƙasa saboda sake gina babban titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙasan ya fitar da kuɗaɗe a kasafin kuɗin 2025 domin kammala aikin.
Shugaba Tinubu ya magantu kan masu sukarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan mutanen da ke sukar gwamnatinsa.
Shugaban ƙasan ya bayyana cewa akwai mutanen da duk abin da zai yi, sai sun ci masa mutunci amma hakan baya damunsa.
Mai girma Bola Tinubu ya nuna cewa akwai muhimman darussa da yake koya daga wajen mutanen da ke zuwa kafafen watsa labarai suna sukarsa.
Asali: Legit.ng