'Ka da Ku Taɓa Shi': Tinubu Ya Yi Ta Maza da Wani Ya Tunkaro Shi yayin Taro a Kaduna

'Ka da Ku Taɓa Shi': Tinubu Ya Yi Ta Maza da Wani Ya Tunkaro Shi yayin Taro a Kaduna

  • Wani mutum da ba a san ko wanene ba ya yi ƙoƙarin kusantar Shugaba Bola Tinubu yayin da yake jawabi a Jihar Kaduna
  • Jami'an tsaro sun dakile lamarin cikin sauri, amma Tinubu ya nuna natsuwa, yana cewa, "Ku bar shi," sannan ya cigaba da jawabi
  • Hadimin shugaban kasa, Otega Ogra ya yabawa jami'an tsaro bisa yadda suka gudanar da aiki ba tare da tangarda ba ga taron ko jawabi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wanene ba ya yi ƙoƙarin kutsawa kusa da Shugaba Bola Tinubu.

Lamarin ya faru ne a yau Alhamis 19 ga watan Yunin 2025 a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya yayin jawabinsa.

Wani ya ratsa jami'an tsaro domin tunkarar Tinubu
Tinubu ya yi ta maza da wani ya tunkaro shi yayin taro a Kaduna. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Punch ta ce shugaban ya kai ziyara Jihar Kaduna domin kaddamar da ayyukan da Gwamna Uba Sani ya aiwatar lokacin da lamarin ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kai ziyara ta musamman jihar Kaduna

Idan ba a manta ba, Tinubu ya ziyarci jihar Kaduna domin ƙaddamar da wasu ayyuka na musamman da gwamna Uba Sani ya yi.

Yayin ziyarar, Tinubu ya karrama tsohon gwamnan Kaduna, Kanal Abubakar Dangiwa mai ritaya da lambar yabo kan jagoranci da kuma gudunmawar da ya bayar.

Ayyukan da aka aiwatar a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Uba Sani sun haɗa da asibiti mai gadaje 300, sababbin tituna a birane da karkara.

Sannan akwai cibiyoyin horo na sana’o’i, da jerin sababbin motoci 100 masu amfani da iskar gas (CNG) domin sauya tsarin sufuri na jihar.

Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Kaduna
Bola Tinubu ya ziyarci jihar Kaduna. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

Yadda wani ya durfafi Tinubu yayin taro

Rahotanni sun ce mutumin ya kusanci Shugaba Tinubu yayin da yake jawabi, lamarin da ya sa shugaban ya dakata na ɗan lokaci cikin mamaki.

Jami'an tsaro na shugaban kasa sun hanzarta dakile mutumin kafin ya kusanci shugaban, tare da kame shi, cewar Channels TV.

Shugaba Tinubu ya nuna natsuwa, inda ya ce:

"Ku bar shi."

Daga bisani, shugaban ya cigaba da jawabin ba tare da wani cikas ba duk da abin da ya faru wanda ya ɗan tayar da hankali.

Hadimin Bola Tinubu a bangaren yada labarai na zamani, Otega Ogra, ya yabawa yadda jami'an suka yi aiki.

Ya ce:

“An gudanar da lamarin cikin ƙwarewa ta jami’an sirri ba tare da ya hana Shugaban kasa ci gaba da jawabi ko taron ba.
“Ku sani cewa, shugaban kasa yana karkashin kulawar ƙwararrun jami’ai daga hukumomin tsaro, leken asiri, da na soji.”

2027: El-Rufai ya yi magana kan zaben Tinubu

Kun ji cewa tsohon gwamna jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce babu wata hanya da Shugaba Bola Tinubu zai bi don komawa mulki.

El-Rufai ya ce 'yan Najeriya sun gaji, kuma gano duk yan siyasar da ke sauya sheka zuwa APC yanzu ba masoyansu ba ne na hakika.

Tsohon gwamnan ya yi hasashen abin da zai faru a zaben 2027 da yawancin 'yan siyasa ke shiri a kai tun yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.