Iran da Isra'ila: Sanata Ya Hango Yakin Duniya na 3, Halin da Najeriya za Ta Shiga
- Tsohon Sanata, Ben Murray-Bruce, ya yi hasashen cewa Yaƙin Duniya na Uku yana tafe, saboda tashin hankali da yawaitar makaman nukiliya
- Ya ce duk da mummunan tasirin da yaƙin zai yi wa duniya, Nahiyar Afirka — musamman Najeriya, za ta tsira saboda rashin sha’awarta kan makaman
- Sanata Murray-Bruce ya ce Najeriya za ta kasance wajen karɓar bakin haure daga kasashen da yaƙin ya shafa, kuma za a karɓe su cikin mutunci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon sanata ne daga jihar Bayelsa, Ben Murray-Bruce ya bayyana cewa duniya na fuskantar barazanar wani sabon Yaƙin Duniya wanda zai fi na baya muni da girma.
A wata hira da ya yi kan harkokin ƙetare a ranar Talata, Murray-Bruce ya bayyana cewa yana ganin duniya na cikin hatsari sakamakon shugabanni marasa sanin ya kamata.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sanatan ya ce ya hango yakin duniya ne saboda yadda makamai masu linzami da nukiliya suka yawaita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, ya bayyana cewa Najeriya da Afirka gaba ɗaya za su tsira daga wannan bala’i saboda matsayinsu na zaman lafiya da rashin tsoma baki a lamarin makaman nukiliya.
“Yakin duniya ba zai shafi Najeriya ba” — Murray-Bruce
Sanata Ben Murray-Bruce ya ce duniya na gab da shiga cikin mummunan rikici, amma Najeriya za ta tsira.
Punch ta wallafa cewa Murray-Bruce ya ce:
“Ina ganin Yaƙin Duniya na Uku yana tafe. Za a fafata ko’ina a duniya, amma mu a Najeriya za mu kasance cikin lafiya.
"Ba mu da niyyar mallakar makaman nukiliya, ba mu da buri na mamaye wani ƙasa, kuma muna zaman lafiya da makwabtanmu na Yammacin Afirka,”
Ya ce kasashen da ke da shugabanni masu yawan amfani da makamai da kuma rashin sanin ya kamata ne za su shiga yakin, amma Najeriya za ta tsaya a gefe tana kallon lamarin.
Sanata Bruce ya ce Najeriya za ta karbi baki
Murray-Bruce ya ci gaba da cewa idan yaƙin ya faru, Najeriya za ta iya zama mafaka ga waɗanda suka rasa matsugunninsu a kasashen yamma.
Ya ce:
“Za mu karɓi Amurkawa, ‘yan Isra’ila da ‘yan Iran. Za mu tabbatar sun samu biza saboda ba ma son su shigo ba bisa ƙa’ida.
"Za mu karɓe su da mutunci kuma su ji daɗin kasancewa tare da mu a Najeriya,”
Wannan furuci ya jawo hankalin mutane da dama, musamman ganin yadda rikicin Iran da Isra’ila ke ƙara ta’azzara a wannan lokaci.

Asali: Getty Images
A karshe, Murray-Bruce ya bayyana cewa dalilin rikice-rikicen duniya ba jama’a ba ne, sai dai shugabanni.
Ya ce:
“Ina ganin shugabanni ne ke haddasa yaƙe-yaƙe, ba talakawa ba. An yi Yaƙin Duniya na farko, na biyu, Yaƙin Koriya, Yaƙin Vietnam, duk saboda shugabanni aka yi su.
"Idan muka ci gaba da zaben shugabanni marasa hankali, to za mu ci gaba da fuskantar yaƙi.”
Putin ya nemi sulhu tsakanin Iran da Isra'ila
A wani rahoto, kun ji cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce zai zamo mai shiga tsakani a yakin da aka fara a Iran da Isra'ila.
Vladimir Putin ya ce yakin zai munana kuma zai shafi kasashe da dama idan Amurka ta yi amfani da karfin soji a kan Iran.
Shugaba Putin ya ce ya yi magana da jagororin kasashen biyu kuma ya bayyana musu cewa zai yi kokarin sulhu a tsakaninsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng