Yakin Duniya Na 3? Yadda Rikicin Iran da Isra’ila Zai Iya Kawo Artabu a Gabas Ta Tsakiya

Yakin Duniya Na 3? Yadda Rikicin Iran da Isra’ila Zai Iya Kawo Artabu a Gabas Ta Tsakiya

  • Tun bayan harin da Isra’ila ta kai wa ofishin jakandancin Iran ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, al'ummar duniya ke tofa albarkacin bakinsu kan abin da zai biyo baya
  • Ana cikin tattaunawa kan lamarin sai zance ya canja bayan da Iran ta kai harin ramuwar gayya wa Isra’ila a ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu
  • Shugabanni da masu sharhi a kan al'amuran yau da kullum sun magantu a kan hatsarin da yaki tsakanin kasashen biyu zai iya haifarwa, ciki har da hasahen yakin duniya na III

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Takaddamar da ta barke tsakanin kasar Isra'ila da Iran na cigaba da jan hankulan al'ummar duniya.

Kara karanta wannan

IMF ta yi hasashen saukar farashin kayayyaki a Najeriya cikin shekarar 2025

Rikicin ya sa mutane da dama ciki har da shugabannin duniya suke hasashen cewa idan yakin ya barke tsakanin ƙasashen biyu zai iya kawo babban tashin hankali a gabas ta tsakiya.

Iran and Israel
Manazarta sun yi hasashen yadda yakin Iran da Isra'ila zai kai ga yakin duniya na III
Asali: Getty Images

Wasu masu sharhi suna ganin illar rikicin ba za ta tsaya a gabas ta tsakiya bane kawai, za ta iya shafan duniya baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙawance tsakanin Isra'ila da Iran

A shekarun baya, kasashen biyu sun kasance kawaye har zuwa juyin juya halin da ya faru a Iran a shekarar 1979.

Wanda ya kawo sabon tsarin mulkin da ya dauki adawa da Isra'ila a matsayin wani muhimmin al'amari, kamar yadda binciken BBC ya tabbatar.

Tun da aka fara zaman doya da manja tsakanin ƙasashen biyu, sun kasance suna nuna wa juna yatsa da cacar baki.

Amma duk da zaman ba ga maciji tsakanin su, ba'a samu kai hari mummuna wa juna ba sai wannan karon.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar kwace lasisin rijiyoyin mai kan rashin biyan haraji

Dalilin fara takaddamar Isra'ila v Iran

Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa, wani jami'in gwamnatin kasar Isra'ila da kuma wani mamba na dakarun sojin Iran sun yi bayani a kan dalilin da ya sa Isra'ila ta kaiwa Iran hari.

A cewarsu, harin da Isra'ila ta kai a birnin Damascus a ranar Litinin ta yi shi ne saboda wani taro da jami'an leken asirin Iran da 'yan gwagwarmayar Falasdinu za su tattauna kan yakin Gaza.

Ko da yake Isra'ila ba ta yi ikirarin kai harin ba, amma kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce Isara'ila na gudanar da ayyukanta a duk fadin yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya kuma kara da cewa Isra'ila ta lashi takobi a kan duk wanda ya ke kokarin zama mata barazana a yankin zai dandana kudarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: EFCC ta bankado wasu makudan kudaden tallafin Korona da aka sace a mulkin Buhari

Wannan ya sa manazarta da dama suke ganin Isara'ila ce ta kai hari ofishin jakadancin Iran a Syria.

Wadanda harin ya ritsa da su

Wadanda suka mutu a harin da Isra'ila ta kai sun hada da Janar Mohamad Reza Zahedi, mai shekaru 65, wanda ke kula da ayyukan soji na Iran a Syria da Lebanon, da wasu janar-janar guda biyu da jami'ai hudu a rundunar Quds, a cewar New York Times.

Martanin da Iran ta yi

Harin ya jawo babbar hasara ga Iran na mutuwar manyan sojojinta ga shi kuma idan ba ta dauki mataki ba, duniya za ta mata kallon zakin roba.

Hakan zai farau ne kasancewar ta dade tana nuna yatsa wa Isra'ila amma ga shi har an watsa mata kasa a ido ta gagara sharewa.

Hakan ya sa tun bayan kai harin, Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Jagoran juyin juya halin Kasar Musulunci na Iran Ayatullah Ali Khamenei ya sha alwashin daukar fansa.

Kara karanta wannan

"Ba mu ciki": Amurka ta bayyana matsayarta kan rikicin Iran da Isra'ila, ta yabawa sojoji

Ga kalamasa kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito:

"Za mu dandanawa gwamnatin Isara'ila kuɗarta ta hannun jajirtattun mazajenmu, za mu sa ta yi nadamar wannan aika-aika da sauran wadanda ta aikata."

-Ayatullah Ali Khamenei, Jagoran juyin juya halin Iran

Iran ba ta tsaya a kumfar baki kawai ba, ta harba makamai masu linzami sama da 300 zuwa Isra'ila a matsayin martani ranar Asabar da ta wuce.

Me Isra'ila ta ce bayan harin Iran?

Hakazalika, bayan ramuwar gayya da Iran ta yi, Isra'ila ta sha alwashin sake kai wa Iran zafafan hare-hare.

Jaridar Times of India ta rawaito Herzi Halevi, babban hafsan hafsan sojin Isra'ila, yana shan alwashin cewa harba makamai masu linzami sama da 300 da Iran ta yi a yankin Isra'ila zai fuskanci martani.

Martanin shugabannin duniya

Bayan da Isra'ila ta furta za ta mayar da martani ga Iran, manyan kasashen duniya sun garagade ta don gujewa abin da zai biyo baya, in ji jaridar the Guardian.

Kara karanta wannan

"Abin takaici ne", Shehu Sani ya magantu game da harin da Iran ta kai kan Isra'ila

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi bayani a kan lamarin a taron gaggawa na kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Lahadi.

Yana mai cewa Gabas ta Tsakiya na dab da kamawa da wuta saboda yaki ta take fama da shi, saboda haka ba za su bari wani yaki ya barke tsakanin kasashen biyu ba

A na shi bangaren, Shugaba Joe Biden ya gargadi Isra'ila kan cewa Amurka ba za ta mara mata baya ba wurin shiga wani yaki da Iran.

Wani babban jami'in gwamnatin Biden ya ce abinda suka sa a gaba shine kwantar da tarzoma a yankin gabas ta tsakiya, ba tayar da yakin da zai zama mafi muni ba.

Da yake mayar da martani kan takaddamar, tsohon sakataren harkokin wajen Birtaniya David Cameron, ya bukaci Isra'ila da ta kai zuciya nesa, kuma kada ta kara ruruta wutar rikici ta hanyar kai wa Iran harin ramuwar gayya.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Jami'in dan sandan da ya yi barazanar sheke farar hula da bindiga ya shiga hannu

Shin rikicin zai kai ga yakin duniya?

Jaridar Economic Times ta ba da rahoton fitacciyar mai hasashe, Baba Vanga, wacce ta yi gargadi mai tsanani game da yuwuwar barkewar yakin duniya na III biyo bayan karuwar tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.

Haka shi ma shugaban Colombia, Gustavo Petro, kamar yadda jaridar Times of India ta ruwaito, ya yi gargadin yiwuwar fara yakin duniya na III daga wannan rikicin.

Ya kuma soki goyon bayan wasu ayyukan kisan kare dangi da manyan kasashen duniya ke yi.

Shugaban ya kara jaddada bukatar daukar matakan samar da zaman lafiya cikin gaggawa daga Majalisar Dinkin Duniya domin kaucewa barkewar yakin duniya na III.

Sakataren tsaron Birtaniya Grant Shapps ya bayyana damuwarsa yana mai cewa duniya na iya shiga babban yaki da zai kai ga yakin duniya.

Wanda ya ke cewa matuƙar ba a dakatar da rikicin ba, akwai yiwuwar barkewar rikice-rikice da za su shafi manyan kasashen duniya kamar China, Rasha, Koriya ta Arewa, da Iran cikin shekaru biyar masu zuwa.

Kara karanta wannan

An sake kai harin da ya yi sanadiyyar kashe mutane 10 a jihar Plateau, jama'a sun shiga firgici

Wanda a cewarsa hakan ba makawa zai kai ga yakin duniya.

Hugh Lovatt, wani babban jami'in siyasa a Majalisar Turai kan Harkokin Waje, ya bayyana wani ra'ayi mai sanyaya zuciya, yana mai cewa abinda ya ke zahiri shine ba za a yi yakin duniya na III ba.

Ya lura da cewa duk da akwai manyan rikice-rikice da tashin hankali a yankuna kamar Ukraine, Gabas ta Tsakiya, da Asiya-Pacific, amma babu alamar cewa za a yi yakin duniya saboda rikice-rikicen a wurare mabanbanta suke faruwa, cewar Times of India.

Me Isra'ila za ta yi yanzu?

Isra'ila dai ta yi alƙawarin mayar da martani, amma wani manazarci, wanda Aljazeera ta ruwaito, ya ce barazanar da Isra'ila ta yi na mayar da martani ga harin na Iran zai iya fuskantar ramuwar gayya kai tsaye daga Iran din.

A wani rahoton na Aljazeera, shugaban Iran ya yi nuni da cewa kai mafi kankantar harin da Isra'ila za ta yi zai haifar da gaggarumin martani daga garesu.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Shekara 1 na Shugaba Tinubu ta fi shekaru 8 na mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

Yanzu idon duniya ya karkata ga kasashen biyu, idan Isra'ila ta mayar da martani, me Iran za ta yi?

Shin idan Iran ta mayar da martani hakan zai kai ga yakin duniya na III? Lokaci alkali, in ji Hausawa.

Najeriya ta magantu akan gabas ta tsakiya

A wani rahoton kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi kira ga ƙasashen Iran da Isra'ila da su sanyawa zukatansu ruwan sanyi biyo bayan harin da aka kai a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu, gwamnatin ta hannun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, ta ba da shawarar hanyar warware rikicin cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel