"Ina da Bidiyo" Sanata Ta Tona Asirin Gwamnan Arewa, Ta Faɗi Yadda Ya Yi Yunƙurin Kashe Ta

"Ina da Bidiyo" Sanata Ta Tona Asirin Gwamnan Arewa, Ta Faɗi Yadda Ya Yi Yunƙurin Kashe Ta

  • Zababbiyar Sanatar Kogi ta tsakiya ta zargi gwamna Yahaya Bello da shirya maƙarƙashiyar kashe ta a lokacin zaɓe a watan Maris
  • Natasha Akpoti-Uduaghan ta kuma maida martani kan kalaman da gwamnan ya yi bayan ta samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara
  • Ta ce tana da kwaƙƙwarar shaida ta bidiyo da ke nuna yadda aka kai mata harin kisa a zaɓen da ya gabata

Jihar Kogi - Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta zargi gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da ƙulla makircin cutar da ita a zaben mambobin majalisar dattawa da aka yi a watan Maris.

Gwamna Yahaya Bello da Sanata Natasha.
Sanata Natasha Ya Zargi Gwamnan APC da Kulla Tugun Kashe Ta a Jihar Kogi Hoto: Yahaya Bello, Natasha Akpoti-Uduaghan
Asali: Facebook

Zababbiyar Sanatar ta yi wannan zargin ne a cikin shirin siyasa a yau na kafar talabijin na Channels ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, 2023.

“Na ji ƙarar bindigogi, na ga ‘yan barandansa suna harbin motata, ina da shaidar bidiyon hakan a tare da ni,” in ji ta.

Kara karanta wannan

FUGUS: Ɗalibai mata na jami'ar arewa da aka ceto daga hannun ƴan bindiga sun samu tallafi mai tsoka

"Sun yi shiga ta rigunan APC, daya daga cikinsu shi ne Amoka, shi ne baturen zaɓen ƙaramar hukumar Okehi. Ya jagoranci gungun ƴan daba suka harbe ni, ina da hoton bidiyon da aka dauka."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta maida martani ga kalaman Yahaya Bello

Sanata Natasha ta kuma nuna damuwa kan kalaman Yahaya Bello na baya-bayan nan cewa ya aminta da nasarar da ta samu a matsayin Sanatar Kogi ta tsakiya.

Ta soki kalaman gwamnan, inda ta nuna tantama kan yadda ake jefa rayuwar mutane cikin hadari tare da bayyana hakan a matsayin ‘kyawun dimokuradiyya.

Natasha ta ƙara da cewa:

“Ya ce wannan ne ƴancin siyasa, ba haka siyasa take ba, ka jefa mutane cikin hatsari, ka sa a yi kisa, lalata kadarori, kuma ka karya tsarin zabe saboda kawai naka ya ci zabe kuma ka kira shi da ‘kyawun dimokradiyya’."

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP za su gana da Ministan Tinubu kan muhimmin batu 1, bayanai sun fito

"Sau biyu na taki sa'a"

Da take jawabi kan nasarar da ta samu a Kotun ɗaukaka ƙara, ta ce duk da hukuncin da aka yanke a farko da ya tabbatar ita ta ci zaɓe, ba ta yi tunanin hakan zai tabbata ba.

Daily Trust ta ruwaito Natasha na cewa:

“Na yi sa’a sau biyu. Har zuwa lokacin da aka bayyana ni a matsayin wadda ta yi nasara, ban da cikakken tabbacin cewa kotun daukaka kara zata tabbatar da haka saboda Najeriya ce, komai na iya faruwa,” inji ta.

Bam ya tashi da masu zuwa jana'iza

A wani rahoton kuma Ana zargin mayaƙan Boko Haram sun dasa wa masu zuwa jana'iza bam a jihar Yobe kuma aƙalla mutane 20 suka mutu nan take.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen sun dawo daga makokin matasa.17 da aka kashe a yankin ƙaramar hukumar Gaidam ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel