Ana Zaman Ɗar Ɗar, Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Gidan Sanata Natasha a Kogi
- Wasu yan bindiga sun sake kai hari gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Kogi inda aka cafke mutum ɗaya da ake zargin yana da hannu
- Rahoto ya ce wanda ake zargi, Joe Suberu, ya amsa cewa wannan karo na uku ne da ya kai hari gidan, an kama shi da adda da da sauran makamai
- Ofishin Sanata Natasha ya ce samamen ya lalata tagogi amma matasan unguwa da 'yan sanda sun kawo dauki har suka fatattaki maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da kama wani mutum bisa zargin hannu a sabon harin gidansu Sanata.
Rundunar ta ce ana zargin wanda aka kaman da hannu a harin da aka kai gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti wanda ba shi ne karon farko ba da lamarin ke faruwa.

Asali: Facebook
Nasarar yan sanda kan harin da aka kai
Kakakin rundunar, SP William Aya, ya tabbatar da hakan ga wakilin Punch, inda ya ce Joe Suberu ya amsa cewa yana daga cikin maharan da suka kai harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama wanda ake zargin, Suberu lokacin harin da ya auku a Ihima, karamar hukumar Okehi a jihar Kogi a ranar Talata, 17 ga Yunin 2025 da muke ciki.
Ya ce:
"Eh gaskiya ne, an kama Joe Suberu a wajen harin. Yanzu haka muna kokarin kama sauran da suka tsere."

Asali: Original
Natasha ta magantu kan barnar da aka musu
A wata sanarwa daga ofishin Sanata Natasha a Abuja, an ce maharan sun lalata tagogi da dama kafin a fatattake su da taimakon jama'a.
Sanarwar ta ce matasa, ‘yan sintiri da ‘yan sanda ne suka hada kai suka hana su ci gaba da barna, inda aka kama Suberu da adda da kayan tsafi.
Har ila yau, an ce Suberu wanda dan asalin yankin ne, ya amsa cewa karo na uku ne da ya shiga irin wannan hari, kuma yana da alaka da siyasa.
Yadda matashi ya tsira daga fushin mutane
Wasu gungun jama’a sun so su kashe Suberu da hannu kafin a ceto shi daga hannunsu yayin da rundunar ta ce sauran maharan na dauke da makamai masu hadari.
Wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari gidan iyayen Sanatan ba, ko a watan Afrilu ma an kai hari amma ba a kama kowa ba, cewar rahoton The Guardian.
Lamarin ya sake tayar da hankulan al'ummar yankin wanda ya saka musu shakku kan yadda ake tafiyar da siyasa da gaba irin haka.
An kuskuri Natasha a harin yan bindiga
Kun ji cewa yan bindiga sun kai hari gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke Obeiba-Ihima, Kogi yayin da dan uwanta ke rangadin duba kwangiloli.
Natasha ta bayyana cewa harin na da alaka da siyasa, inda ta bukaci sufeton ‘yan sanda ya dawo da jami’an tsaronta da aka janye mata bayan dakatar da ita.
Sanatar ta zargi shugaban majalisar dattawa, tsohon gwamna Yahaya Bello da Gwamna Usman Ododo da hannu idan wani abu ya same ta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng