Majalisar Amurka na Shirin ba Trump Kunya kan Shiga Fadan Iran da Isra'ila
- Wasu 'yan majalisar Amurka daga jam’iyyu biyu sun gabatar da kudirin doka domin hana amfani da sojojin Amurka a yaki da Iran ba tare da amincewar su ba
- Kudirin ya samu goyon bayan wasu 'yan majalisa, inda suka ce tsarin mulkin Amurka bai ba shugaban kasa shi kadai damar kaddamar da yaki da wata kasa ba
- 'Yan majalisun sun jaddada cewa Amurkawa ba sa bukatar sake fadawa cikin wani sabon yaki a Gabas ta Tsakiya wanda zai haifar da bala’i a fadin duniya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - A ranar Talata, wasu ‘yan majalisar wakilai guda biyu daga jam’iyyun Republican da Democrat a Amurka sun gabatar da kudirin doka kan yakin Iran da Isra'ila.
An gabatar da kudirin ne domin hana amfani da dakarun Amurka a yakin da bai samu izinin majalisa ba, musamman dangane da Iran.

Asali: Getty Images
TRT World ta wallafa a Facebook cewa Dan majalisa, Thomas Massie daga jam'iyyar Republican ne ya jagoranci gabatar da kudirin tare da hadin gwiwar dan Democrat, Ro Khanna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin, wanda ke da cikakken iko, zai iya zuwa dandalin majalisa don muhawara da kada kuri’a bayan kwanaki 15 ko da kwamitin bai dauki mataki ba.
'Majalisa ne da ikon ayyana yaki' - Massie
Massie ya bayyana cewa tsarin mulkin Amurka bai ba wa shugaban kasa ikon kaddamar da yaki da wata kasa mai cin gashin kanta ba, matukar ba ta kai hari kan Amurka ba.
Dan majalisar ya ce:
“Majalisa ce kadai ke da ikon ayyana yaki.
"Wannan yakin da ke tsakanin Isra’ila da Iran ba namu ba ne. Amma ko da namu ne, dole ne majalisa ta yanke hukunci bisa tsarin mulki,”
A shafin X, Thomas Massie ya yi magana game da yunkurin da suke yi a majalisa na adawa da shigar Amurka yakin Israila da Iran.
'Ba a bukatar wani sabon rikici' - Khanna
Ro Khanna ya ce bai kamata wani shugaban kasa ya tsallake majalisa wajen yanke hukuncin shiga yaki ba, ya jadda wannan a X a jiya.
Aljazeera ta wallafa cewa ya kara da cewa mutanen Amurka ba su son a jefa su cikin wani sabon rikici mai hadari a Gabas ta Tsakiya.
“Ina alfahari da jagorantar wannan kudiri tare da Massie domin tabbatar da ikon majalisa a lamurran yaki.
"Dole ne duk wani yunkurin soji a kan Iran ya samu amincewar majalisa,”
"Yan majalisa da suka goyi bayan kudirin
Wasu fitattun ‘yan majalisa da suka kasance masu goyon bayan kudirin sun hada da Alexandria Ocasio-Cortez, Ilhan Omar, Rashida Tlaib, Jim McGovern, Ayanna Presley, Pramila Jayapal.
Kudirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin tasirin rikicin Isra’ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Asali: Getty Images
A yanzu haka ana cigaba da samun fargaba kan yiwuwar fadada rikicin har ya shafi sauran kasashe kamar Amurka.
Iran ta gano mafakar Isra'ila aTehran
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta sanar da gano wani gida da ta ce ana amfani da shi wajen ajiyar kayan leken asirin Isra'ila.
An ruwaito cewa bayan bincike mai zurfi, Iran ta tabbatar da kama mutane kusan 30 da ake zargi na da alaka da Isra'ila.
Hukumomi a kasar Iran sun sanar da 'yan kasar matakan da ya kamata su dauka wajen gano masu tallafawa Isra'ila da bayanai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng